Home Back

YAJIN AIKI: A ɗaga wa aikin jigilar Alhazai Ƙafa – NAHCON

premiumtimesng.com 2024/7/3
ƘARANCIN KUƊI: Hukumar Alhazai ta rage ƙuɗin da take baiwa ma’aikatan wucin gadin da na hukumar da ke aikin Hajji bana

Wani baban jami’i a Hukumar Alhazai ta ƙasa Dakta Sa’idu Dumbulwa ya yi kira ga kungiyar Kwadago ta koma teburin shawara ta duba maganar jigilar Alhazai da ake kokarin Kammalawa nan da kwanaki 7 masu zuwa.

Dumbulwa ya ce kungiyar Kwadago bata tsara yajin aikin ba yadda ya kamata ganin cewa akwai yiwuwar a samu matsaloli masu yawa idan ba a magance yajin aikin ba da wuri musamman wanda ya shafi jigilar Alhazai da ake yi a yanzu.

” Duk da cewa tabbas suna da damar shiga yajin aiki idan basu gamsu da gwamnati ba amma kuma ai akwai musulmai da yawa a kungiyar da ya kamata a ce sun yi dubi da haka kafin su fara yajin aikin.

” Aikin Hajji lamari ne mai matuƙar mahimmanci ga musulmai. Ba zai yiwu a ce saboda irin wannan abu ba a samu matsala wajen ganin aikin ya tafi kamar yadda aka tsara shi.

” Saboda haka ina kira ga kungiyar Kwadago da su sake yin nazari kan lamari tunda wuri.

Hakazalika shima shugaban hukumar NAHCON Jalal Arabi ya yi kira ga kungiyar Kwadago ta sake yin dubi ga lamarin domin muddun aka samu matsala abin ba zai yi wa Alhazai daɗi ba da ita kanta hukumar, harda gwamnati baki ɗaya.

Zuwa yanzu dai hukumar Jin daɗin alhazai ta kwashi sama da mutum 30,000 zuwa ƙasa mai tsarki cikin mutum 65,000 daga Najeriya.

Shima shugaban MURIC, Ishaq Akintola, ya gargaɗi Kungiyar Labour da ta shiga taitayinta’ domin Babban Sallah ya na tafe sannan ga aikin Hajji da ake ta kokarin kammala wa.

Ya ce ” Saboda rashin kangado da sanin ya kamata, sai a wannan lokaci da ake ta fafutuka da shirye shiryen Sallah babba, shine za su wani fara yajin aiki na gamagari.

People are also reading