Home Back

'Yan Kwadago Na Shirin Ɗaukar Mataki Bayan Gwamnatin Tinubu Ta Miƙa Tayin N62,000

legit.ng 2024/7/2

FCT Abuja - Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan sabon mafi ƙarancin albashi ya ƙarƙare zaman tattaunawa a ranar Jumu'a, 7 ga watan Yuni, 2024.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Bayan shafe sa'o'i ana tattake wuri, kwamitin ya bayar da shawarin N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.

Shugabannin NLC da TUC.
NLC na iya komawa yajin aiki bayan ta yi watsi da sabon tayin N62,000 Hoto: Nigeria Labour Congress HQ Asali: Facebook

Jaridar Leaderhship ta tattaro cewa ƴan kwadago sun fatali da sabon tayin, inda suka jaddada cewa sun rage bukatarsu zuwa N250,000.

Amma gwamnatin tarayya da kamfanoni masu zaman kansu sun amince da N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Da alamu dai rashin jituwar na iya tilastawa kungiyoyin kwadago NLC da TUC, su sake farfado da yajin aikin da suka sassauta na mako guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC na duba yuwuwar sake koma yajin aikin wanda ta ɗage na tsawon kwanaki biyar bayan gwamnati ta tsaya kan sabon tayin.

Ku saurare mu....

Asali: Legit.ng

People are also reading