Home Back

Bam Ya Hallaka Jami'an CJTF 5 a Jihar Borno, Wasu Sun Samu Raunuka

legit.ng 2024/5/20
  • Wani bam da ƴan ta'addan ISWAP suka dasa a kan hanya ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan aƙalla jami'an tsaro CJTF guda biyar a jihar Borno
  • Jami'an suna kan hanyarsu ta zuwa aikin sintiri ne lokacin da motarsu ta taka bam din bisa kuskure a kusa da ƙauyen Gajibo
  • Wasu daga cikin jami'an da harin ya ritsa da su sun samu raunuka inda aka garzaya da su zuwa asibiti domin ba su kulawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Aƙalla jami’an Civilian Joint Task Force (CJTF) biyar ne suka rasa ransu a jihar Borno.

Jami'an na CJTF sun rasa ransu ne bayan sun taka wani bam da ƴan ta’addan ISWAP suka binne a ƙaramar hukumar Dikwa ta jihar Borno.

Bam ya kashe jami'an CJTF a Borno
Jami'an CJTF sun rasu a wani harin bam a Borno Hoto: @govborno Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a kusa da ƙauyen Gajibo da misalin ƙarfe 12:30 na rana a ranar Asabar, 27 ga watan Afirilun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Jami'an tsaron dai sun rasu nan take lokacin da suka taka bam ɗin wanda ƴan ta'addan suka binne lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa aikin sintiri.

Wani majiyar tsaro ya bayyana cewa:

"An dasa bam a wajen ƙauyen Gajibo cikin ƙaramar hukumar Dikwa wanda ya hallaka aƙalla jami'an CJTF guda biyar, yayin da wasu suka samu munanan raunuka."

Wani babban kwamandan CJTF a Maiduguri ya tabbatar da aukuwar harin, inda ya ƙara da cewa jami'an suna kan hanyar aikin sintiri ne lokacin da suka taka bam ɗin bisa kuskure a kusa da ƙauyen Gajibo a ranar Asabar.

Ya ce wasu mambobinsu sun rasu amma bai bayyana adadinsu ba.

Mutum nawa bam ya raunata?

Zagazola Makama wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce majiyoyi sun bayyana cewa wasu mutum uku da abin ya shafa sun samu raunuka daban-daban.

Waɗanda suka samu raunuka a cewar majiyoyin an kwashe su zuwa asibiti, yayin da jami'an CJTF takwas da suka rasu aka kai su ga iyalansu domin yi musu jana'iza.

An kashe ƴan ta'adda a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya da aka tura domin yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso Gabas sun kashe ƴan ta'adda biyu a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe ƴan ta'addan ne yayin da suke kan hanyar zuwa kai farmaki a kauyen Mashurori.

Asali: Legit.ng

People are also reading