Home Back

RA’AYIN PREMIUM TIMES: YAJIN AIKI: Me ya sa gwamnati ta ƙi koyon yadda ake sasantawa ne?

premiumtimesng.com 2024/6/28
JANYE YAJIN AIKI: Gwamnati da Kungiyar Kwadago sun cimma matsayar wucin-gadi

An jefa Najeriya cikin duhu a daren Litinin ta makon jiya, daidai ƙarfe 2:19 na dare, yayin da ma’aikata masu yajin aiki suka katse tashar wutar lantarkin ƙasar nan baki ɗaya.

Hakan harkokin zirga-zirgar jiragen sama, asibitoci, kotuna, bankuna da makarantu, har da ɗalibai masu rubuta jarabawar WASC duk yajin aikin sai da ya shafe su.

Ofisoshin gwamnati ciki har da na Abuja duk sun kasance a garƙame, lamarin da ya nuna irin mumnunan tasirin da yajin aikin ya yi. Gwamnati fa ta na girbar wa kanta da ‘yan Najeriya matsalar tattalin arziki ba gaira ba dalili, saboda rashin iya riƙon ragamar shugabanci.

Tun tuni sai da ƙungiyoyin ƙwadago suka bayar da wa’adin kwanakin da suke so a yi masu ƙarin albashin nan, amma gwamnati ba ta yi da gaske ba.

Maganar gaskiya ‘yan Najeriya fama da ƙuncin raɗaɗin tsadar rayuwa tun daga ranar da Shugaba Bola Tinubu ya kama mulki, ranar 29 ga Mayu, 2023, sakamakon cire tallafin fetur, karya darajar Naira waɗanda suka kwashe ƙafafuwan tattalin arzikin Najeriya ya yi faɗuwar da ya kasa tashi, kuma aka rasa masu iya tayar da shi.

Tun daga lokacin ƙuncin rayuwa, fatara da talauci suka baibaye ‘yan Najeriya. Marasa galihu suka riƙa dogara da ɗan abincin tallafin da ake ba su na cin yau da na gobe, amma ba zai iya kai su jibi ba. Su kan su marasa galihun ƙalilan ne ke iya samun abincin. Wani ma har ya gama rayuwar sa ba zai taɓa ganin wanda ya samu tallafin ba.

Shugaban NLC da na TUC sun je taron sasantawa da gwamnati a ranar 28 ga Mayu, 2024, amma wakilan gwamnati ko gwamnoni babu wanda ya halarta. Hakan ya nuna gwamnati ba gaske take yi ba, kuma ba ta san abin da take yi ba dangane da batun ƙarin mafi ƙanƙantar albashi.

Da farko ƙungiyar ƙwadago ta nemi a biya Naira 494,000 mafi ƙanƙantar albashi, a daidai lokacin da wata jiha ta bayyana Naira 70,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi. Ita kuma gwamnatin tarayya ta ce Naira 48,000 za ta iya biya. Aka yi ta ja-in-ja, har dai gwamnatin tarayya ta ce za ta biya Naira 60,000. Ƙungiyar ƙwadago ta yi fatali da wannan tayin farashin, wanda a ranar Juma’a kuma aka yi ƙari zuwa Naira 62,000, amma ƙungiyar ƙwadago ta ce Naira 250,000 ta ke so a biya mafi ƙanƙantar albashi.

Shugaban NLC Ajaero ya zargi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila da laifin ko-in-kula, wanda ya ce tun cikin shekarar da ta gabata ya ke ta yi wa lamarin tangal-tangal.

Bayan cire tallafin fetur, maganar gaskiya ministocin ƙwadago da Tinubu ya naɗa, wato Solomon Lalong da Nkeiruka Onyejeocha, ba su cancanta ba.

Wannan yajin aiki da aka yi kwanaki biyu aka janye, ya haifar tsaida tattalin arzikin Najeriya cak. Ya ka ke tunani idan da an shafe sati ɗaya ana yajin aikin? Kuma har yanzu gwamnatin tarayya ba ta ɗauki darasin komai ba.

Bai kamata har yanzu an kasa tsaida kyakkyawan albashi ba, amma a kamfaci har Naira biliyan 57 a sai wa ‘yan majalisa motoci ba. Haka shi ma Shugaban Ƙasa da matar sa, an ware masu Naira biliyan 28 domin sayen motocin su. Ga gidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, wanda aka ware wa Naira biliyan 21 da sauran taɓargaza da almubazzaranci daban-daban da wannan gwamnatin ke yi da kuɗaɗe.

Gwamnonin Najeriya 30 sun kashe Naira biliyan 986.64 wajen shaye-shaye da ciye-ciyen kayan alatu na tanɗe-tanɗe da lashe-lashe a cikin watanni ukun farkon shekarar 2024. Amma kuma sun murje idanu sun fito sun ce ba su iya biyan Naira 62,000 mafi ƙanƙantar albashi.

Ya kamata dai gwamnati ta tashi tsaye domin shawo kan wannan matsala a daidai lokacin da malejin tsadar rayuwa da na yi tsadar kayan abinci da kayan masarufi ya cilla sama da tsawo ko tsallen da talaka zai iya yi ta taɓo farashin.

Ƙanana da matsakaitan ma’aikata na cikin sahun gaban talakawan ƙasar nan. A gaggauta duba lamarin da tabaran hanyen nesa, ba a riƙa kallon matsalar ta cikin madubin duba-rudu ba.

People are also reading