Home Back

Ambaliyar ruwa na addabar kudancin Jamus

dw.com 2024/7/1
Ambaliyar ruwa a Nordendorf na Jamus
Ambaliyar ruwa a Nordendorf na Jamus

Tun da misalin karfe shida na safiyar Asabar din da ta gabata mazauna karamin garin Nordendorf da ke arewacin birnin na Augsburg suka tsinci kansu cikin mummunan rudani.

Magajin garin na Nordendorf da ke da yawan al'umma dubu biyu da 600 Tobias Kunz da sauran al'ummarsa, sun shiga cikin tashin hankali tare da neman shawo kan ambaliyar ruwan.

Da tallafin ma'aikatan sa-kai kimanin 300, sun yi kwashe ceto dalibai 'yan makarantar firamare tare da kai su tudun-mun tsira. A hirarsa da tashar DW, Magajin garin na Nordendorf Tobias Kunz ya shaidar da cewa

"Mun cika buhunhuna kimanin dubu 40 da kasa, domin toshe hanyar da ruwan ke biyowa. Mun yi kokarin dakile kwararasa a kusan mita 240, sai dai bai yi wani tasiri sosai ba kasancewar madatsar ruwan ta tumbatsa sakamakon mamakon ruwan sama da ake ci gaba da yi tamkar da bakin kwarya. Muna dai kokarin shawo kan matsalar, koda yake ba mu shirya mata ba.

Abin farincikin shi ne, mun samu taimako sosai daga al'umma. Kamfanoni da daidaikun jama'a sun taimaka sosai, muna alfahari da hakan. Muna ta aiki ba dare ba rana, wasu sun kwashe tsawon sa'o'i kusan 40 ba tare da sun rintsa ba."

Ambaliyar ruwan ta fi shafar jihohin Baden-Württemberg da Bavaria, jami'in kashe gobara guda ya rasa ransa yayin da mutum guda ya yi batan dabo. Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Diedorf Philipp Niegl ya bayyana cewa sun aike da sakon gargadi ga mazauna yankin ya kara da cewa.

"Sakon gargadin da muka aike ya taimaka gaya, a hannu guda kuma manhajar gargadi ta Nina ta bayar da sanarwa kan kwashe al'umma. Mun kuma kunna kararrawar gargadi kan annoba, a daidai lokacin da gargadi kan fashewar madatsun ruwan ta fita. Mun samar da abubuwa da dama da za su taimaka wajen kwashe mutane, motar da za a iya tuka ta a cikin ruwa mai zurfi da muka samar ta taimaka gaya wajen kwashe mutane."

Koda yake makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe a garin Nordendorf, sai dai abin da ya fi damun magajin garin Tobias Kunz shi ne yadda suka gaza kwashe kayan da ke filin wasan na makarantar da aka kashewa kudi kimanin Euro miliyan daya. Halin da ake ciki a yanzu haka a garin na Nordendorf dai, shi ne al'ummomi da dama ke cikinsa a kudancin Jamus.

Madatsun ruwan ba za su iya jure mamakon ruwan saman da ake yi a yankunan ba, wanda aka bayyana cewa ruwan da ya sauka cikin sa'o'i 24 a wasu yankunan ya kai kimanin wanda ya sauka a cikin wata guda. An kwashe mazauna kauyuka da dama, sakamakon ruwan saman kamar da bakin kwarya da rabon da aga irinsa an kai tsawon shekaru 100.

People are also reading