Sallar Layya: Masana sun Bayar da Hanyoyin Cin Nama ba Tare da Matsala ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Yayin da musulmi ke cike da farin ciki ana ta soyawa da tsiren naman layya da aka yanka domin ibada, masana a bangaren cimaka sun yi gargadina a bi dokokin kare lafiya.
Dietician Auwal Aliyu Ahmad da ke Kano ya bayyana cewa duk da yanzu lokaci ne da nama ya wadata ba kamar kullum ba, za a iya samun cututtuka da dama idan ba a dauki wasu matakai ba.
Masanin cimakan ya shaidawa Legit Hausa yadda ya kamata a dauki matakan kare kai idan ana son a kammala sallah ciki lafiya baka lafiya ba tare da barkewar cututtuka ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dietician Auwal Aliyu ya shawarci musulmi su guji cin nama da yawa, sannana su rika bayar da tazara a tsakanin lokutan da su ka ci nama saboda ya narke yadda ya kamata.
"Akwai lokacin da ya ke dauka kafin ya narke a cikin ciki, kamar ya na daukan awa takwas zuwa awa 12 ba kamar sauran abinci ba da ya ke daukan kila awa uku zuwa hudu.
- Dietician Auwal Aliyu Ahmad
Ya ce idan aka ci nama har ya yi yawa, akwai yiwuwar kamuwa da amai da gudawa da lalacewar ciki, sannan rashin sarrafa shi da kyau ka iya janyo kamuwa da kwayoyin cututtuka.
Likita a asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, Dr. Sani Giade ya shawarci musulmi su tabbata sun wanke dabbobin layyarsu da kyau domin tsira da lafiyarsu bayan sallah.
Vanguard News ta wallafa cewa ya a guji soya naman rumumus saboda hakan ya na cire alfanun da ke jikinsa, musamman ga masu ajiye naman na tsawon lokaci.
A baya mun kawo labarin yadda wasu su ka rufe idanunsu tare da sace ragon limamin kauyen Mista Ali da ke karamar hukumar Bussa ta jihar Filato gabanin yanka.
Malam Haruna Yakub ya yi shelar sace masa ragon bayan ya kammala limancin sallar idi tare da bayyana mamakinsa kan yadda lalacewar ta kai har da sace masa ragon layya.
Asali: Legit.ng