Home Back

Ramadan: Gwamnan Kebbi Ya Kaddamar Shirin Rabon Kayan Abinci

leadership.ng 2024/4/29
Ramadan: Gwamnan Kebbi Ya Kaddamar Shirin Rabon Kayan Abinci

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kaddamar da shirin rabon kayan abinci na watan Ramadan, domin a rage radadin wahalhalu ga al’ummar jihar.

Gwamnan, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabinsa na kaddamar da rabon abincin don ci gaban manufofin jin-kai na gwamnatinsa.

A yayin da yake bayyanawa taron jama’ar cewa” gwamntinsa ta yi hakan ne daga jama’a don taimaka wa mabukata da kuma bayar da agaji ga wadanda matsalolin zamantakewa da tattalin arziki ya shafa.

“Hanya ce ta nuna hadin kai da goyon baya ga jama’a da kuma yadda za su iya samun albarkatu don ci gaban rayuwarsu.

“Wannan alama ce ta al’umma da kuma zama majibincin ɗan uwan juna.”

A cewar gwamnan, rabon hatsin shi ma wani mataki ne na wucin gadi na samar da tallafi ga al’ummar jihar baki daya.

Ya kuma umarci duk wadanda aka damka wa hatsin da su tabbatar an bai wa daukacin al’ummar jihar kasonsu.

Ya kara da cewa, “Gwamnatin Jihar Kebbi ita ce gwamnatin al’umma, don haka ya kamata a raba kayan abinci ba tare da nuna bambancin addini ko kabilancin ba.

“Siyasa ta kare, an gama zabe, abin da ya rage shi ne shugabanci na gari, bai kamata a bar kowa ba, babu bambancin jam’iyya.

Ya kuma gargadi kwamitocin rabon kayayyaki a dukkan matakai kan duk wani nau’i na mataki kar a siyar da su, ko kuma karkatar da hatsin da aka yi tanadi don mutanen jihar.

Ya kuma yi gargadin cewa duk wani jami’in gwamnati da aka samu yana karkatar da hatsi za a hukunta shi, wanda zai kai ga tsige shi daga mukaminsa, ya kuma umarci shugabannin hukumomin tsaro da su tabbatar da bin ka’ida gaba daya ko kuma a kama duk wanda aka samu da laifi a hukunta shi.

Tun da farko kwamishinan noma, Alhaji Shehu Mu’azu ya yaba wa gwamnan bisa amincewa da sayan buhunan iri-iri domin jin dadin jama’arsa.

Ya kuma yaba da kyawawan halayen Gwamna Nasir Idris zuwa ga jama’ar jih6ar Kebbi kan wannan tsari da ya kaddamar na rabon abinci a duk fadin jihar.

Mu’azu ya sanar wa mahalarta taron cewa abin da aka kaddamar don rabawa kashi ashirin ne na hatsin da gwamnati ta saya yayin da za a yi rabon sauran a ma’auni daga baya a matakai.

Ya ce tuni aka aike da hatsin da ke tara a dukkanin kananan hukumomin 21 zuwa hedikwatar kananan hukumomin don raba wa ga al’ummar yankunan.

Daga karshe Kwamishinan ya bayyana irin kayan abincin da gwamnatin jihar ta sayo don rabawa ga watan azumin Ramadana sun hada da Gero, dawa da kuma shinkafa da sauransu.

 
People are also reading