Gwamnan Edo: PDP Ta Ce An Toshewa APC Hanyar Maguɗi, Ta Fadi Yadda Za Ta Ci Zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Shugabannin jam'iyyar PDP sun yi gangami yayin da zaɓen gwamna a jihar Edo ke kara matsowa kusa.
Jam'iyyar PDP ta ce a wannan karon za ta tabbatar da samun nasara kan APC a jihohin Edo da Ondo.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri da muƙaddashin shugaban PDP, Iliya Damagun ne suka yi bayanin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake bayani, gwamnan jihar Adamawa ya bayyana cewa sanya kimiyyar zamani cikin harkokin zabe zai hana yin maguɗi.
Ahmadu Fintiri ya kara da cewa suna da kwarin gwiwa a kan dan takararsu na jihar Edo saboda ayyukan cigaba da ya kawo jihar.
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP, Iliya Damagun ya ce shugaba Bola Tinubu ba zai yi tasiri a zaben jihar Edo ba.
Damagun ya bayyana haka ne inda yake cewa dama tun asali akwai taken cewa jihar Edo ba Legas ba ce kuma hakan zai yi aiki a wannan karon.
Shugaban PDP ya kara da cewa a wannan karon jam'iyyar ta shirya tsaf domin samun nasara a zaben da za a gudanar, rahoton Punch.
Ambasada Damagun ya kuma tabbatarwa jam'iyyar APC cewa abu ne mai matukar wahala gareta ta samu jihar Edo musamman yadda dan takarar PDP ya samu karɓuwa.
A ranar 21 ga watan Satumba mai zuwa ne hukumar INEC ta ayyana cewa za a yi zaben gwamna a jihar Edo.
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana aniyarta na samun karin gwamnonin jihohi a kudancin Najeriya.
Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a birnin Kalaba.
Asali: Legit.ng