Home Back

EFCC Ta Gurfanar da Ma'aikacin Gwamnati Gaban Kotu Saboda Zargin Hana Bincike

legit.ng 2024/7/3
  • Wani ma’aikacin gwamnatin jihar Gombe, Usman Mallam ya gurfana gaban kotu bayan zargin da hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ke yi masa
  • Hukumar EFCC na zargin Usman Mallam, wanda ke aiki a ofishin sakataren gwamnatin jihar Gombe da keta takardun binciken almundahana da ya biyo ta ofis dinsa
  • Bayan ya musanta zargin, Babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar karkashin mai shari’a TG Ringim ta bayar da balin wanda ake kara kan N10,000,000 da karin sharadi daya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe- Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta zargi ma’aikaci a ofishin sakataren gwamnatin jihar Gombe, Usman Mallam da yaga wasu wasikar bincikenta.

Hukumar ta gurfanar da Mallam gaban babbar kotun tarayya bisa zarginsa da kokarin kawo cikas ga binciken da EFCC ke yi kan zargin almundahana da yiwa tattalin arziki ta’annati.

Hukuma
EFCC ta gurfanar da Usman Mallam gaban kotu Hoto: Economic and Financiall Crimes Commission Asali: Facebook

A sakon da EFCC ta wallafa a shafinta na facebook, laifin da ake zargin Mallam da aikatawa ya saba da sashe na 38 (1) na hukumar, kuma sashe na 38 (2) (a) da (b) ya tanadi hukuncin laifin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC: Kotu ta bada belin Usman Mallam

Bayan gurfanar da Usman Mallam gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta Gombe kan tuhumar kekketa takardun bincike da hukumar EFCC, ya musanta zargin.

Bayan musanta zargin da ake yi masa ne lauyan EFCC, AM Labaran ya shaidawa ya nemi kotu ta sanya ranar fara sauraron karar. domin fara sauraron shari'a.

Punch News ta wallafa cewa lauyan wanda ake kara, SS Usman ya roki kotu ta ba wanda ya ke wakilta beli, lamarin da mai shari’a TG Ringim ya amince da shi.

Daga sharuddan belin akwai biyan N10, 000,000 da gabatar da mutum guda da zai tsaya masa daga ma’aikatar gwamnati ko kamfani mai zaman kansa, sannan aka dage shari’ar zuwa 9 Yuli, 2024.

Korar shugaban EFCC: Kotu ta yanke hukunci

A wani labarin mun kawo yadda babbar kotun tarayya ta yi watsi da karar da ke naman a kori shugaban hukumar yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) Ola Olukoyede daga kujerarsa.

A karar da wani lauya, Victor Opatola ya shigar gaban kotun, ya na rokon a kori Mista Olukoyede daga mukaminsa saboda a cewarsa, bai cancanci rike mukamin ba.

Asali: Legit.ng

People are also reading