Home Back

Iyayen Yaron Da Aka Kashe A Makarantar Sojin Sama Sun Bukaci A Yi Adalci

leadership.ng 4 days ago

Iyalan marigayi mataimakin shugaban daliban makarantar sakandare ta Rundunar Sojin Sama da ke Kaduna, Felid Blaise, wanda ake zargin wasu daliban aji shida (SS3) ne suka kashe a dakin kwanan makarantar sun yi kira da a yi musu adalci. 

Wani daga cikin kawunnen marigayin mai suna Paul ya magantu game da mutuwar marigayin dalibin wanda kuma shi ya bukaci yin adalcin.

Mista Paul ya ambata wannan bukata ne a Kaduna a lokacin da yake zantawa da manema labarai inda ya bayyana cewa marigayi Felid kanensa ne kuma maraya da ya rasa iyayensa biyu a shekarar 2013.

Ya ci gaba da cewa, abin da ya fi dacewa da mahukuntan makarantar da rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) za su iya yi don karrama marigayin shi ne kara kaimi wajen bankado abin da ya kai ga mutuwarsa.

Ya bayyana cewa ya ga marigayi Felid cikin koshin lafiya a lokacin da ya ziyarce shi a yayin hutun Sallah, ya kara da cewa mutuwar yaro haziki kuma mai tarbiyya ya jefa kansa da iyalansa baki daya cikin dimuwa.

Ya ce sakataren ilimi na sansanin sojin sama ne ya sanar da iyalan rasuwar dan uwansu.

“An tabbatar mana da cewa a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don zakulo wadanda suka aikata laifin da kuma ganin an yi adalci.

“Mu a matsayinmu na danginsa mun amince da amincin makarantar da kuma rundunar sojojin sama, kuma muna da yakinin cewa wadanda suka kashe danmu ba za su tsira daga hukunci ba,” in ji Paul.

Rundunar sojin saman Najeriya ba ta bayyana sunan wanda aka kashe da kuma musabbabin mutuwarsa ba, amma ta sanar da cewa a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da kwakkwaran bincike domin gano abin da ya kai ga mutuwarsa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar, Air Bice Marshal Edward Gabkwet, a wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ya fitar ya ce, “Shugaban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hasan Abubakar, da daukacin jami’an NAF na cike da alhini wannan lamari mai radadi da bakin ciki da ya faru na mutuwar daya daga cikin dalibanmu a makarantar sakandaren sojojin sama, Kaduna.”

People are also reading