Home Back

Tobi Amusan ta samu galaba a tseren gudun mita 100

rfi.fr 2024/5/5

'Yar wasan tsaren Gudun Famfalaki Tobi Amusan, ta samu Galaba a tseren gudu na Mita 100, cikin dakika 12 da digo 89.

Wallafawa ranar: 22/03/2024 - 13:13

'Yar wasa Tobi Amusan
'Yar wasa Tobi Amusan © REUTERS - MIKE SEGAR

Wannan nasarar itace ta bata damar zama Zakarar gasar a jere har karo Uku.

A baya dai ta lashe gasar a kasar Congo Brazaville a shekarar 2015, sai a birnin Rabat na kasar Morocco a shekarar 2019 kana yanzu a birnin Accra na kasar Ghana.

Haka zalika shi ma Dan wasan Najeriya Joseph Amoah, ya jagoranci kasar wajen lashe Lambar Zinare kan kasar Ghana, a Gudun karba-karba na Canji wato Relay, Inda kasar ta Ghana ta zo ta Biyu, sai Liberia da ta kare a mataki na Uku.

People are also reading