Home Back

Ba Zan Taba Iya Aure Ko Zama Da Wanda Ba Ya Son Sana’ar Dana Ke Yi Ba -Asmee Wakili

leadership.ng 2024/5/8
Ba Zan Taba Iya Aure Ko Zama Da Wanda Ba Ya Son Sana’ar Dana Ke Yi Ba -Asmee Wakili

Jarumar fina finan Hausa na Kannywood Asmau Wakili wadda aka fi sani da Asmee Wakili a wani faifan bidiyo da ta dora a kan shafinta na Tik Tok ta bayyana cewar ba za ta iya zama da duk wanda ba ya son sana’ar da take yi ba.

Wasu na kallon sana’a fim a matsayin wata sana’a da ba za su iya zaman aure da duk wani wanda yake cikin harkar ba, hakan ya sa jarumai a masana’antar kan fito fili su nuna cewa suma haka abin yake a wajensu domin kuwa kowa tashi ta fishshe shi.

Asmee Wakili jarumar Kannywood ce wacce ta shahara a wannan kafa musamman fannin raye-raye inda take fitowa a manyan fina finai tana tikar rawa tare da abokan aikinta, hakan ya sa ta tara dimbin masoya masu shaawar kallon wakokin da take fitowa a cikinsu.

People are also reading