Home Back

Fifikon Manzon Allah (SAW): Darasi Daga Suratun Najmi (1)

leadership.ng 2 days ago
Raudar manzo

‘Yan’uwa Musulmi Assalamu alaikum warahmtullahi Ta’ala wa barkatuh. Barkan mu da sake haduwa a wannan darasi namu mai albarka game da abubuwan da suka shafi janibin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (SAW).

A wannan makon, za mu cigaba da darasin ne a kan ayoyin da suke nuna fifiko da girman Manzon Allah (SAW). Koda yake Alkur’ani dukkansa girman Annabi yake nunawa. Allah Tabaraka Wata’ala a cikin Alkur’ani ya saukar da Suratun Najmi, farkon ayar, “Wannajmi izhaa hawae…..” har zuwa “lakad ra’e min ayati rabbihil kubre”, wanda muke son bayani a ciki. Amma kafin nan, ita wannan surah ita ce sura ta farko da Manzon Allah (SAW) ya karanta ta a sarari a garin Makkah. Kafin lokacin, ko Alkur’ani ya sauka sai dai a rika karantawa a boye saboda mutanen gari (kafiran Makkah).

Sayyidina Abdullahi bin Mas’ud (RA) yana daga cikin makaranta Kur’ani har ma Manzon Allah (SAW) ya ce “duk mai son ya karbi Kur’ani danyensa ya karba a wurin Abdullahi bin Mas’ud”. To shi wannan Sahabin ya tambayi Manzon Allah ya yi ma sa izini ya je tsakiyar Makkah ya karanta Alkur’ani. Manzon Allah ya ce ma sa “ka yi hakuri, Allah zai kawo wannan rana”. Toh, shi dai yana so a ransa. Shi kuma mutum ne gajere kwarai da gaske mara jiki (RA), amma kuma malami ne makaranci. Ya zo ya fara karanta Kur’ani a fili sai Abu Jahli ya zo ya tattaka shi har sai da Abbas ya zo ya kwace shi, da ya zo ya fada wa Annabi (SAW) sai ya ce ma sa “ai na fada ma (tukuna)”. Da lokacin karantawa a fili ya zo, wannan surah ta “wannajmi” ita Manzon Allah (SAW) ya fara karantawa a fili. Kuma su kafiran Makkah suka tsokano ta, domin sun ce suna zaton Annabi kage ya yi wa Allah da ya ce abin da yake karantawa daga Allah ne. Shi ne sai Allah ya tsarkake Manzon Allah daga abin da suke jingina ma sa. Allah ya yi rantsuwar cewa shi ne ya aiko shi da Alkur’anin nan kuma Manzon Allah ba ya fadar abin da ba shi ne ya yi ma sa wahayi ba. Shaidodi masu kyau Allah ya yi wa Manzon Allah (SAW) kuma ya fito ya karanta. Sannan wani gamo-da-katari a lokacin da ya karanta duk mazajen Makkah suna wurin. Saboda mu’ujizar Kur’ni da fasahar karatun da yadda abin ya fi karfin hankalin su (kafiran), a lokacin da Annabi (SAW) ya gama karanta surar ya yi sujuda sai da kowa da kowa (musulmi da kafiran) suka yi in ban da Umayyatu bin Khalf, amma shi ma sai da ya debi kasa ya sa a goshinsa domin ya ce ba zai yi wannan abin (sujada) da aka yi ba, wai don kar duwawunsa ya zama a sama kansa kuma yana kasa. Ma’ana shi ba zai dora duburarsa a kan kansa ba.

Surar kamar yadda ta fara da “Wannajmi”, Allah ya yi rantsuwa da Tauraron Surayya. Masu sanin ilimin Falaki sun san kan wannan tauraron. A can cikin Suratud Darik ma Allah ya yi rantsuwa da shi wurin da ya ce “Ina rantsuwa da wannan tauraro mai haske”. Allah ya yi ranstuwa da Tauraron Surayya a lokacin da ya fadi. A aya ta biyu, Allah ya ce “(Wallahi) Abokin nan naku (Muhammadu) bai bace ba, bai yi jahilci ba (irin malamin da ya sani kuma ya take sani)”. Ma’ana ayar tana mayar wa da kafiran martani ne cewa Manzon Allah (SAW) ba ya jahilci cikin abin da yake fadi, kuma bai zama wanda ya sani ya take sani ba. Ko kuma Manzon Allah bai yi ko da kuskure cikin abin da yake isarwa na sakon Manzanci daga Allah ba.

Ayar gaba ta ci gaba da cewa “(Annabi SAW) ba ya furuci a bisa son rai. Face abin da aka yi wahayi izuwa gare shi”. Wato Alkur’ani da wannan shari’a da Manzon Allah yake isarwa babu wani abu na son rai a ciki illa wahayin da Allah yake yi masa. Sannan wanda aka aiko ya sanar da shi wahayin Mala’ika ne mai tsananin karfi na zahiri. Mai tsananin karfi na badini ko kuma a wata fassarar a ce mai tsananin kyau wato Jibrilu AS.

Mala’ika Jibrilun ya daidaita a mahudar rana (fassara ta farko). Mala’ika Jibrilu (AS) a cikin sifar mutum yake zuwa wurin Manzon Allah (SAW). Wata rana Manzon Allah ya tambaye shi yadda sifarsa ta Mala’ika take, bayan ya gaya masa, sai ya ce yana so ya gan shi a sifar, shi kuma ya ce “ka fada wa Ubangijinka idan ya yi izini in nuna ma”. Manzon Allah (SAW) ya roka, Allah Ta’ala ya yi mai izini. Mala’ika Jibrilu ya ce masa ya bar Makkah ya fito zuwa Dutsen Kogon Hira, sannan Mala’ika Jibrilu ya bayyana masa yana da fukafuki dubu dari shida. Kuma ko wane fuffuke guda daya ya rufe mahudar rana da mafadarta. Ko ganin Jibrilu kadai ai ya fi karfin hankali ballantana da irin wannan idon namu. Amma kuma sai ga shi Allah ya nuna wa Manzon Allah Jibrilu a sifarsa ta Mala’ika.

Ayar ta cigaba da cewa Jibrilu ya daidaita yana sasanni madaukaki a mahudar rana. Sannan ya kusanta zuwa ga Annabi (SAW), ya kara kusanta a gare shi dai har ila yau. Sai da ya zama tsakaninsa da Manzon Allah ya zama kamar tankwaren baka ko ya fi haka (fassara ta farko tana nuni ne ga cewa Mala’ika Jibrilu ne ya kusanci Manzon Allah). Sai Allah ya yi wa Bawansa wahayin abin da ya yi ma sa. Zuciyar Manzon Allah (SAW) ba ta karyata abin da ya gani ba. Sau da yawa mutum zai iya ganin abu amma da ya fadi wa mutane suka karyata shi zai iya dagewa kan abin, ya ce ko da dai ku kun karyata, idona ya riga ya gani. Manzon Allah zuciyarsa ba ta karyata abin da idonsa ya gani ba (SAW).

Allah ya tambayi kafiran Makkah cewa “yanzu kwa dinga jayayya da shi a kan abin da ya gani (SAW)? Ai ya gan shi (Mala’ika Jibrilu AS) ma a wani karon. Nan ga Magaryar Tikewa”. An ce abin da ya sa aka ambaci Magaryar Tikewa da wannan sunan shi ne duk ilimin wani Halittar Allah a nan ya kare. Nan ne bakin bodar halitta duka in ban da Manzon Allah (SAW), shi ne kadai ya taba tsallaka ta. Shi ya san meye a bayanta. Shi ya san abin da ya gani, ya iya fadar wani, wani kuma kirjinsa ne kadai ya iya dauka. Don haka ake ce mata Magaryar Tikewa. Aljannar Makoma a nan wurin (Magaryar) take. “Yayin da abin da ya lullube wannan bishiya ya lullube ta. Idon Manzon Allah bai karkace ba (ya kasa ganin abin). Kuma bai shige abin da ake nema ba (ma’ana ya ga abin da aka nema ya gani daidai). Hakika (wallahi) Manzon Allah ya ga wasu ayoyin Ubangijinsa masu girma”.

Wadannan su ne ayoyi goma sha takawas na “wannajmi” da muka kawo bayanansu a sama. Daga ayoyi masu girman da Allah ya ce ya gani; malamai sun ce ya ga Rafrafu (Shimfida ce kuma Mala’ika ce koriya) wadda ta rufe duk iyakar sasannin da ya gani.

A ranar Isra’i, Manzon Allah (SAW) ya hau abubuwan hawa kala-kala. Daga Makkah zuwa Baitul Makdisi ya hau Buraka aka tuka shi (SAW). Ana zuwa Baitul Makdisi ya daure Burakar, ta gama aikinta. Daga nan kuma ya hau Mi’iraji (kamar misalin lifter ko kumbo apolo ko dai makamantansu na wannan zamanin), an ce da Mi’iraji ne Allah yake daukan ran Mumini a yi sama da shi. Saboda kyan abin sai ka ga idon mutum da bakinsa sun bi suna kallo, domin bai taba ganin irin sa ba. Idan rai ya fita kuma bakin da idon ba za su iya rufewa ba har sai an rufe wa mutum wani zubin, kamar dai yadda idan dan kauye ya ga wani abin mamaki da bai taba gani ba. To wannan Mi’iraji ke nan.

Bayan Manzon Allah ya hau Mi’iraji har zuwa Magaryar Tikewa, amfani da Mi’iraji ya kare. Daga nan kuma Mala’ika Jibrilu (AS) ya tsaya; ya ce Manzon Allah ne kadai ya isa ya tsallaka wannan waje. To daga nan ne sai wannan shimfida ta Rafrafu ta dauke shi zuwa inda Allah ya so. Don haka, Manzon Allah ya ga Rafrafu, ya ga Jibrilu, ya ga Al’arshi, ya ga Kursiyyu, ya ga Magaryar Tikewa, ya ga Mustawad Darafaini (wani irin waje ne da misali idan ka yi kudu sai ka fito yamma, idan ka yi sama sai ka fito kasa, abu ne da ya fi karfin hankali). Kuma duk wannan Manzon Allah ya yi ne da jikinsa ba wai a barci ba, a’a, da jikinsa da ransa duk gaba daya (SAW).

Ayoyin wannajmi ke nan da muka dauka a wannan darasin domin yin nazarin girman darajarsa (SAW). A mako mai zuwa insha Allahu za mu tashi da bayani a kan me ya sa aka ce Manzon Allah (SAW) ya ga wasu ayoyi ne daga cikin ayoyin Ubangijinsa?

Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.

People are also reading