Home Back

Kane ya kafa tarihin yawan cin kwallaye na kashin kansa

bbc.com 2024/5/10
Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Harry Kane ya ci kwallo biyu a Bayern Munich da ta doke Eintracht Frankfurt 2-1 a Bundesliga, ya kafa tarihin yawan cin kwallaye da yawa a kaka na kashin kansa.

Mai shekara 42 ya ci kwallo 42 a dukkan karawa a bana tun bayan da ya fara yi wa Bayern wasa a kakar nan, wanda ya taba zura 41 a raga a Tottenham a 2017/18.

A gasar ta Bundesliga ta mako na 31 ranar Asabar, Kane ya fara cin kwallo a minti na tara da fara wasa, sannan ya ci na biyu a bugun fenariti a zagaye na biyu.

Tun kan hutu Eintracht Frankfurt ta zare daya ta hannun Hugo Ekitike.

Kawo yanzu Kane ya ci kwallo 400 jimilla tun daga kungiyoyin da ya buga wa tamaula da kuma tawagar Ingila.

Ya zura kwallo a ragar kungiya 16 daga 17 da ya fuskanta a Bundesliga a kakar nan, ya yi kan-kan-kan a bajintar da Gerd Müller (1966-67 & 1969-70), Ailton (2003-04) da Robert Lewandowski (2019-20 and 2020-21).

Kane shi ne na farko da ko dai ya ci kwallo ko ya bayar aka zura a raga a dukkan karawa 17 a kakarsa ta farko a Bundesliga.

Freiburg ce kungiyar da Kane bai ci ba, wadda ya bayar da kwallo aka zura mata a raga a cikin watan Oktoba.

Kane dan wasan tawagar Ingila, na bukatar cin kwallo shida nan gaba, domin ya kafa tarihin Robert Lewandoewski da ya zura 41 a raga a Bundesliga, kuma saura wasa uku a kare kakar nan.

Bayern Munich tana ta biyu a teburin Bundesliga da tazarar maki 11 tsakani da Bayern Leverkusen, wadda ta dauki kofin babbar gasar tamaula ta Jamus a karon farko a tarihi.

People are also reading