Home Back

Hukumar Shirya Jarabawa JAMB Ta Saki Sakamakon Jarabawar UTME 2024

legit.ng 2024/5/18
  • Sakamakon jarabawar share fagen shiga manyan makarantun gaba da sanadire (UTME) wanda ɗalibai suka kammala ya fita
  • Hukumar da ke da alhakin shirya jarabawar (JAMB) ce ta bayyana sakon sakamakon ɗalibai 1.94 da suka zana jarabawar a bana 2024
  • Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da haka yayin hira da ƴan jarida a hedkwatar JAMB da ke Bwari a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar da ke shirya jarabawar share fagen shiga manyan makarantu (JAMB) ta saki sakamakon dukkan ɗaliban da suka zauna jarabawar a 2024.

Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Ishaq Oloyede, ne sanar da sakin sakamakon jarabawar UTME a taron manema labarai a hedkwatar JAMB da ke Bwari a Abuja.

Shugaban JAMB, Ishaq Oloyede.
Jarabawar JAMB ta shekarar 2024 ta fito ranar Litinin Hoto: JAMB Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an fara zama jarbawar ne a ranar Jumu'a, 19 ga watan Afrilu kuma an kammala a ranar Litinin 29 ga watan Afrilu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton Punch, JAMB ta yi jinkirin sakin sakamakon jarabawar ne domin ƙara nazari da bincike da tsefe sakamakon don kar a samu matsala.

Hukumar ta yanke shawarin ƙara kwanaki kafin fitar da sakamakon jarabawar domin tabbatar da gaskiya game da zargin wani ya zana ma wani da sauran laifukan satar amsa.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading