Back to the last page

Mataimakin Atiku, Tambuwal, Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Lallaba Sun Gana da Obasanjo

legit.ng 6 hours ago
  • Abokin takarar Atiku Abubakar, Gwamna Okowa na jihar Delta ya jagoranci jiga-jigan jamiyyar PDP sun sa labule da tsohon shugaban kasa Obasanjo
  • Darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a PDP, Gwamana Aminu Tambuwal na cikin wakilan da suka je Abeokuta ranar Asabar
  • Ana hasashen dai wannan ziyara ba zata rasa alaka da rigingimun cikin gida da suka hana PDP zaman lafiya ba

Ogun - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta ya jagoranci wakilan jam'iyyar sun sa labule da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta ranar Asabar.

Sauran tawagar wakilan sun haɗa da Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa a PDP, Gwamna Aminu Tambuwal na Sakkwato da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido.

Wakilan PDP a gidan Obasanjo.
Mataimakin Atiku, Tambuwal, Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Lallaba Sun Gana da Obasanjo Hoto: premiumtimesng Asali: UGC

Mai taimakawa tsohon shugaban kasa kan harkokin watsa labarai ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar sakamakon rashin sanin yan jarida gabanin fara taron.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Arewa Ya Lallaba Patakwal, Ya Sa Labule da Wike

A cewar sanarwa, taron wanda ya gudana a sirrance ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyintola, tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da kuma d'an kasuwa, Oyewole Fasawe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar Pemium Times ta tattaro a cikin sanarwan gwamna Tambuwal na cewa jirgin tawagar wakilan ta dira Abeokuta ne domin kai ziyarar girma ga tsohon shugaban kasa, inda ya kara da cewa sun tattauna batutuwa masu amfani.

Gwamna Tambuwal ya kara da cewa:

"Sako na ga yan Najeriya shi ne su fito kwansu da kwarkwata idan ranar zabe ta zo a watan Fabrairu su dangwalawa tikitin da ya hada yan takarar da suka yi dai-dai da al'adar kasar nan, wadanda zasu kafa gwamnatin da zata hada kan kasa."
Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kirstocin Arewa Sun Yanke Shawarar Atiku Zasu Marawa Baya - Dogara

"Kuma ta farfado da tattalin arzikin mu kana ta kara dankon zumunci a tsakanin yan kasa, ba kowane tikiti nake nufi ba illa na Atiku Abubakar da gwamana Okowa."

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan taro na kus-kus ba zai rasa alaka da rigingimun da suka ki ci suka ki cinyewa ba a PDP tun bayan kammala zaben fidda dan takarar shugaban kasa

Tsagin G5 karkashin jagorancin gwamana Nyesom Wike ya bukaci shugaban PDP na kasa, Dakta Iyrchia Ayu ya yi murabus kana a maye gurbinsa da wani dan kudancin Najeriya, channels ta ruwaito.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP a jihar Bauchi ta yi biyayya ga hukuncin Kotu, ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani a mazaɓar Bauchi ta kudu

Ɗan takarar da ya lashe zaben fidda gwanin farko na tikitin takarar Sanatan Bauchi ta kudu a inuwar PDP, Alhaji Garba Ɗahiru, ya ƙara samun nasara a karo na biyu.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya ce ba zai yi muhawara da dan takarar wata jam'iyya ba sai ya cika sharudda 4

Bayan Kotun ta rushe zaben farko, sakamakon sabon zaɓen da aka gudanar ya nuna Ɗahiru ke kan gaba da kuri'u 71, ya lallasa sauran abokan hamayyarsa.

Asali: Legit.ng

Back to the last page