Home Back

EURO2024: Yadda duk da cika bakin ƴan ‘Premier League’, Sifaniya ta nuna musu ruwa ba tsaran kwando bane

premiumtimesng.com 2024/8/22
EURO2024: Yadda duk da cika bakin ƴan ‘Premier League’, Sifaniya ta nuna musu ruwa ba tsaran kwando bane

Tawagar Ƙasar Sifaniya ta samu nasarar lashe kofin Nahiyyar Turai na 2024 da aka kammala a kasar Jamus a ranar Lahadi.

Tawagar ta samu wannan nasarar ne bayan doke ƙasar Ingila a wasan ƙarshe da ci 2-1.

Da wannan nasarar Sifaniya ta zama ƙasa ta farko da ta fara lashe gasar cin kofin nahiyar Turai karo hudu a tarihi

Nico Williams da Mikel Oyarzabal ne suka zurawa Sifaniya kwallayen, ɗan wasan Ingila Cole Palmer ne ya samu nasarar warware ma ta kwallon ɗaya a lokaci ana ci ɗaya da nema.

Da wannan sakamakon Sifaniya ta lashe Euro 2024, kuma na huɗu jimilla, ita ce ke kan gaba a yawan ɗaukar kofin nahiyar Turai a tarihi.

Sifaniya ta fara lashe kofin nahiyar Turai a 1964 da 2008 da 2012 da kuma yanzu a 2024 a Jamus.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da Ingila ta kai wasan karshe a Euro, bayan da Italiya ta doke ta a wasan karshe na Euro 2020 a bugun fenariti a Wembley.

Haka kuma karon farko da Ingila ta yi wasan karshe a babbar gasa ba a gida ba, wadda take da kofin duniya a 1966, sai dai ba ta taɓa lashe Euro ba.

People are also reading