Home Back

Kotu ta fara sauraron ƙarar da Alhaji Aminu Ado Bayero ya maka gwamnatin Kano da kwamishinan ƴan sanda

dalafmkano.com 2024/7/4

Babbar kotun tarayya mai lamba 3 da ke zamanta a jihar Kano, karkashin jagorancin Justice Abobeda, ta fara sauraran wata Shari’a wadda Alhaji Aminu Ado Bayero ya shigar, yana ƙarar gwamnatin Kano da kwamishinan yan sanda da kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano.

Tun da farko mai ƙarar ya nemi kotun da ta hana gwamnatin Kano da ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro kama shi ko kuma tsangwamar sa.

A zaman kotun na yau da ke ci gaba da gudana, lauyan gwamnatin Kano Barista Mahmud Magaji SAN, ya shaidawa kotun cewar mai ƙarar a lokacin da ya shigar da ƙarar ba shine sarkin Kano ba, domin dokar da ta kafa shi ta riga ta rushe shi.

Lauyan ya ci gaba da cewa, kuma majalisar dokokin Kano ita ce tayi dokar da aka nada shi a matsayin Sarki a karkashinta, yanzu kuma majalisar ta soke dokar kuma dama aikin majalisa kenan suyi doka ko kuma suyi wa dokar gyara.

Mahmud Magaji ya roki kotun da tayi watsi da karar sakamakon bata da hurumi ya kuma kafa hujja da Shari’ar sarkin Muri da gwamnatin jahar Gongola, a nan ne lauyan mai ƙara ya yi suka.

Tun dai da safiyar Juma’ar nan ne aka girke jami’an tsaro da suka zagaye hanyoyin kotun domin samar da tsaro.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa, yanzu haka kotun na ci gaba da sauraron ƙarar.

People are also reading