Home Back

Arangamar Ƴan shi’a da ‘yan sanda ya yi sanadiyar rayukar Ƴan shi’a huɗu, Ƴan sanda uku sun jikkata a Kaduna

premiumtimesng.com 2024/5/6
Arangamar Ƴan shi’a da ‘yan sanda ya yi sanadiyar rayukar Ƴan shi’a huɗu, Ƴan sanda uku sun jikkata a Kaduna

Ƴan kungiyar Shi’a hudu sun rasu bayan wata arangama da suka yi da ‘yan sanda a Kaduna ranar Juma’a.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safe a lokacin da ‘yan kungiyar ta IMN ke gudanar da tattaki domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a rikicin da ake ci gaba da yi a Gaza da Isra’ila.

A cewar shugabannin IMN, wasu mambobi 20 sun samu raunuka a yayin arangamar.

Shugaban kungiyar ta IMN, Aliyu Turmizi, ya ce suna gudanar da zanga-zangar lumana ne domin nuna goyon baya ga al’ummar Gaza, kamar yadda wasu kasashen yammacin duniya ke yi don nuna adawa da rikicin Gaza.

Ya ce muzaharar tasu ta kasance cikin lumana amma ‘yan sanda sukan kai musu hari kamar yadda ya faru a yau Juma’a.

A cewarsa, kungiyar na ci gaba da tattara sunayen wadanda aka kashe, inda ta sha alwashin cewa kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da nuna kiyayyarsu ga Isra’ila kan abin da suke yi wa Falasdinawa.

Sai dai rundunar ‘yan sandan ta musanta kashe wani dan kungiyar, inda ta bayyana cewa jami’ansu ba su yi amfani da harsashin gaske ba wajen tarwatsa gungun masu zanga-zangar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mansir Hassan, ya ce ‘yan sanda uku sun samu raunuka yayin da suke kokarin tarwatsa muzaharar ta IMN.

Ya kara da cewa sun samu bindigogi kirar hannu, da wasu makamai tare da masu mzaharar.

People are also reading