Home Back

Bude Iyakokin Nijeriya Da Nijar: NIS Ta Dage Takunkumin Shige Da Fice

leadership.ng 2024/4/29

ACG Sunday James Ya Garzaya Yankin Yobe Da Borno Don Tabbatarwa

Bude Iyakokin Nijeriya Da Nijar: NIS Ta Dage Takunkumin Shige Da Fice

Sakamakon umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar na sake buɗe iyakokin Nijeriya da Nijar, Shugabar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa,  CGI Kemi Nanna Nandap ta Umarci dukkan kwanturololin jihohi da na kula da iyakoki da ke gefen iyakokin Nijeriya da Nijar su tabbatar da aiwatarwa.

Shugabar hukumar ta umarci kwanturololin su ɗage takunkumin shige da ficen mutane da kayayyaki a iyakokin.

Hukumar ta NIS ta tabbatar wa da al’umma cewa a shirye take wajen kula da shige da fice a kan iyakokin Ƙasa bisa ƙa’ida tare da kiyaye mutunci da tsaron iyakokin Nijeriya.

Babban Shugaban Shiyya ta Uku (Zone C), da ta kunshi jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Yobe da Filato, Mataimakin Kwanturola Janar (ACG) James Sunday, ya kai ziyarar aiki a jihohin Borno da Yobe da ke Arewa maso Gabas domin lura da yadda ake bude iyakar.

nijar

CGI Kemi Nanna Nandap

A cewar ACG Sunday James, ya garzaya sansanonin gudanar da ayyukan hukumar domin ganin an dauki matakin da ya dace na tabbatar da bude iyakokin ga jama’a ba kuma tare da kawo matsala ga tsaron kasa ba.

A cewar ACG Sunday James, “An sanar da Kwanturola na Yobe da Borno kan wannan umarni, na zo nan a matsayina na shugaban shiyyarsu domin tabbatar da cikakkiyar aiwatar da umarni, tare da tabbatar wa jama’a jajircewarmu wajen tabbatar da tsaron kasa ta hanyar shige da ficen iyakoki a kan ka’ida domin kiyaye mutunci da tsaron ‘Yan Nijeriya.

nijar
Tawagar ACG Sunday James tare da Gwamna Buni da manyan jami’an Gwamnatin Yobe

A ranar Laraba ne gwamnatin tarayyar Nijeriya ta umurci hukumomin tsaron kan iyakokin da abin ya shafa da su bude kan iyakar Nijeriya da Nijar a wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Ajuri Ngelale ya Sanya wa hannu.

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin Nijeriya ta kasa da ta sama da jamhuriyar Nijar tare da dage wasu takunkumin da aka kakabawa kasar nan take.

A cewar sanarwar ta Ajuri Ngelale, umarnin ya yi daidai da shawarar da Kungiyar ECOWAS ta yanke a babban taronta na musamman da ta yi a ranar 24 ga watan Fabrairun 2024 a Abuja.

nijar

Shugabannin ECOWAS sun amince da dage takunkumin karya tattalin arziki da suka kakaba wa Jamhuriyar Nijar, Mali, Burkina Faso, da Guinea.

Daga cikin takunkuman da aka kakaba wa Jamhuriyar Nijar da shugaban kasa ya ba da umarnin dagewa nan take, akwai:

(1) Rufe iyakokin kasa da ta sama tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar, da kuma hana zirga-zirgar jiragen sama a yankunan kasashen ECOWAS daga Nijar zuwa cikinsu ko daga cikinsu zuwa can.

(2) Dakatar da duk wasu hada-hadar kasuwanci da hada-hadar kudi tsakanin Nijeriya da Nijar, da kuma dakatar da duk wasu ayyuka na musamman kamar samar da wuta lantarki ga Jamhuriyar Nijar.

nijar

(3) Rufe kadarorin Jamhuriyar Nijar a Babban Bankin ECOWAS da kadarorin kasar na kamfanonin gwamnati, da ma’aikatu a bankunan kasuwanci.

(4) Dakatar da bai wa Nijar duk wani tallafi na kudi da mu’amala da duk hukumomin kudi, musamman.

(5) Hana tafiye-tafiye ga jami’an gwamnati da iyalansu.

 
People are also reading