Home Back

RAHOTON BINCIKE: Yawan fama da Zazzabin cizon sauro na haddasa hawan jini da ciwon zuciya

premiumtimesng.com 2024/7/2
Mosquito
Mosquito

Rahoton wata sabuwar bincike da ‘Lancet Global Health Journal’ ta fitar ya nuna cewa mutum na iya kamuwa da ciwon hawan jini da ciwon zuciya a dalilin yawan kamuwa da zazzabin cizon sauro.

Cibiyar Lancet Global Health Journal ya gabatar da wannan bincike bayan wasu kwararru masu gudanar da bincike 10 sun gabatar da sakamakon binciken su dake tabbatar da haka.

Binciken duk da cewa yana bukatan a ci gaba da gudanar da bincike ya nuna cewa mazauna Kudu da Saharar Afrika da India ne za su fi kamuwa da wadannan cututtuka saboda yaduwar zazzabin cizon sauro a yankunan.

Binciken ya kara nuna cewa mutum zai iya kamuwa da wadannan cututtuka idan tun yana yaro yana yawan fama da zazzabin cizon sauro.

Lancet Global Health Journal ta yi kira da a zurfafa bincike musamman yadda sakamakon binciken zai taimaka wajen gano sabon hanyoyin dakile yaduwar zazzabin cizon sauro, cututtukan dake kama zuciya da yawan jini.

Yaduwar hawan jini a duniya

Lancet Global Health Journal ya nuna cewa daga shekarun 2009 zuwa 2019 an samu karin kashi 100% a yawan mutanen dake kamuwa da hawan jini a duniya.

Sakamakon bincike ya nuna cewa cutar ta fi yaduwa a kasashe masu tasowa.

Rahotannin sun nuna cewa kasashen dake Kudu da Saharar Afrika da India na daga cikin wuraren da cutar ta fi wa katutu a duniya.

Akalla mutum daya cikin mutanen 10 a Kudu da Saharar Afrika na suke da cutar sannan a India mutum daya cikin mutanen uku.

Zuwa yanzu mutane masu shekaru 20 zuwa 40 a wadannan kasashen duniya ne suka fi kamuwa da hawan jini.

Yaduwar Zazzabin cizon sauro

Duk shekara akalla mutum miliyan 200 ne ke kamuwa da zazzabin cizon sauro inda daga cikin rabin miliyan rabin miliyan na mutuwa sannan kashi 90% daga cikin mutanen dake kamuwa da yawan dake mutuwa duk daga kasashen Kudu da Saharar Afrika suke.

Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO ta ce akalla mutum miliyan 244 ne suka kamu da cutar a 2021 sannan a 2022 mutum miliyan 249.

WHO ta ce cutar ta yi ajalin mutum 610,000 a 2021 sannan a 2022 mutum 608,000 a duniya.

Zazzabin cizon sauro ya fi yaduwar a kasashe kamar su Najeriya, Jamhuriyar kasar Kongo, Uganda da Mozambique.

Cutar ta yi ajalin kashi 11% na mata masu ciki da kashi 25% na yara kanana.

People are also reading