Home Back

Hakkin Bil Adam Gata Ne Ga Wasu A Amurka Karkashin Ra’ayin Wariyar Launin Fata

leadership.ng 2024/7/5
Hakkin Bil Adam Gata Ne Ga Wasu A Amurka Karkashin Ra’ayin Wariyar Launin Fata

Wata cibiya mai nazarin harkokin kiwon lafiya ta jami’ar Rutgers ta kasar Amurka ta ba da kididdiga a kwanan baya cewa, Amurkawa ‘yan asalin Afirka da yawansu ya kai a kalla kashi 60% suna fuskantar hare-haren bindiga a kasar, kuma yawancinsu suna zama ne a unguwannin masu karamin kudin shiga. Abin takaici shi ne, wata hukumar masana mai zaman kanta ta kasa da kasa dake karkashin majalisar kula da harkokin hakkin dan Adam ta MDD, ta ba da rahoto cewa, ra’ayin nuna bambancin launin fata ya kutsa kai cikin aikin ‘yan sanda da ma tsarin shari’a na kasar Amurka. Yiwuwar mutuwar Amurkawa ‘yan asalin Afirka sakamakon hare-hare daga ‘yan sandan kasar ya ninka sau 3 bisa na fararen fata, kuma adadin ya ninka sau 4.5 a fannin tsare su a gidan kurkuku. Ban da wannan kuma, ana nuna bambancin launin fata mai tsanani a fannin ba da jiyya, inda yawan mutuwar mata bakaken fata masu juna biyu, ya ninka sau 3 bisa na fararen fata. Ban da Amurkawa ‘yan asalin Afirka, al’ummomi ‘yan asalin Latin Amurka da Asiya, su ma sun dade suna fama da wannan matsala, wadanda ba a iya tabbatar da tsaronsu yadda ya kamata. ‘Yan siyasar Amurka su kan yi shelar cewa, su ne masu kare hakkin Bil Adam, amma a wani bangare na daban, sun kawar da ido daga matsalar nuna bambancin launin fata suna take hakkin sauran mutane da kafafunsu, har hakkin ya zama gata ga wasu mutane kalilan a Amurka. (Mai zane da rubutu: MINA)

People are also reading