Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Neman Tumbuke Ododo Daga Kujerar Gwamna
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta dauki mataki kan shari'ar zaben jihar Kogi.
Kotun ta tanadi hukunci a shari'ar da ɗan takarar SDP, Murtala Ajaka ke kalubalantar zaben wanda Usman Ododo ya yi nasara.
Alkalan kotun guda uku sun tanadi hukunci tare da tabbatar da tuntubar bangarorin biyu kan ranar sake zama kan dambarwar zaben, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan masu kara, Pius Akubo ya bukaci kotun ta rusa hukuncin karamar kotu tare da tabbatar da Ajaka wanda ya lashe zaben.
Akubi ya ce hukuncin karamar kotun da ta tabbatar da nasarar Ododo ya saba ka'idojin shari'a.
A martaninsa, Cif Kanu Agabi da ke bangaren hukumar INEC ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar Ajaka kan soke zaben da aka gudanar a jihar.
Har ila yau, lauyan Ododo, Joseph Daudu ya ce babu gamsassun hujjoji kan korafin da SDP ta shigar.
Daudu ya kuma bukaci kotun ta yi watsi da korafi kan takardun bogi da ake yi kan Ododo inda ya ce matsala ce kafin zaɓe.
A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta yi hukunci kan rigimar sarauta da aka daɗe ana yi a jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya.
Kotun ta yi fatali sa korafin Michael Onakoya da aka tube a matsayin Sarkin Agbooye da ke Ipe a jihar shekaru da suka wuce
Onakoya tun farko ya bukaci kotun ta yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara tare da mayar masa da kujerarsa na sarauta.
Asali: Legit.ng