Home Back

Kotu Ta Tanadi Hukunci Kan Shari'ar Neman Tumbuke Ododo Daga Kujerar Gwamna

legit.ng 2 days ago
  • Yayin da ake ci gaba da shari'a kan zaben gwamnan jihar Kogi, Kotun Daukaka Kara ta yi zama kan dambarwar
  • Kotun ta tanadi hukunci kan shari'ar da Murtala Ajaka na SDP ke kalubalantar zaben da aka gudanar a watan Nuwambar 2023
  • Hakan ya biyo bayan tabbatar da Usman Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta dauki mataki kan shari'ar zaben jihar Kogi.

Kotun ta tanadi hukunci a shari'ar da ɗan takarar SDP, Murtala Ajaka ke kalubalantar zaben wanda Usman Ododo ya yi nasara.

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamna Kogi
Kotun Daukaka Kara ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kogi. Hoto: Usman Ododo, Murtala Ajaka. Asali: Twitter

Ododo: Matakin da kotun ta ɗauka

Alkalan kotun guda uku sun tanadi hukunci tare da tabbatar da tuntubar bangarorin biyu kan ranar sake zama kan dambarwar zaben, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan masu kara, Pius Akubo ya bukaci kotun ta rusa hukuncin karamar kotu tare da tabbatar da Ajaka wanda ya lashe zaben.

Akubi ya ce hukuncin karamar kotun da ta tabbatar da nasarar Ododo ya saba ka'idojin shari'a.

Lauyan Ododo ya roki kotu alfarma

A martaninsa, Cif Kanu Agabi da ke bangaren hukumar INEC ya bukaci kotun ta yi watsi da bukatar Ajaka kan soke zaben da aka gudanar a jihar.

Har ila yau, lauyan Ododo, Joseph Daudu ya ce babu gamsassun hujjoji kan korafin da SDP ta shigar.

Daudu ya kuma bukaci kotun ta yi watsi da korafi kan takardun bogi da ake yi kan Ododo inda ya ce matsala ce kafin zaɓe.

Kotu ta yi hukunci kan rigimar sarauta

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta yi hukunci kan rigimar sarauta da aka daɗe ana yi a jihar Lagos da ke Kudancin Najeriya.

Kotun ta yi fatali sa korafin Michael Onakoya da aka tube a matsayin Sarkin Agbooye da ke Ipe a jihar shekaru da suka wuce

Onakoya tun farko ya bukaci kotun ta yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara tare da mayar masa da kujerarsa na sarauta.

Asali: Legit.ng

People are also reading