Babban Dan Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da mutuwar babban ɗan tsohon gwamnan Oyo, Kolapo Ishola.
Marigayin mai suna Kunle Kolapo ya rasu da safiyar yau Laraba 3 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Leadership ta tattaro cewa marigayin kafin rasuwarsa lauya ne kuma ya tsohon kwamishina a jihar.
Kunle ya rike mukamin kwamishinan ne a mulkin tsohon gwamnan jihar, Otunba Christopher Alao-Akala.
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a bayyana musabbabin mutuwar babban ɗan tsohon gwamnan ba.
Har ila yau, iyalan basu fitar da wata sanarwa ba a hukumance kan babban rashin da suka tafka.
Tsohon gwamnan ya mulki jihar Oyo ne daga shekarar 1991 zuwa 1993.
Daga bisani, Isola ya rasu a ranar 9 ga watan Agustan shekarar 2011 yana da shekaru 77 a duniya.
A wani labarin, kun ji cewa wani matashi mai suna Ufuoma ya hallaka mahaifinsa wanda Fasto ne a jihar Delta a yau Laraba.
Marigayin mai suna Issac Umurie ya rasa ransa ne yayin da yake tsaka da bacci da tsakar daren yau Laraba 3 ga watan Yulin 2024.
Matashin har ila yau, ya farmaki mahaifiyarsa yayin da yake kokarin kare mijinta da kuma dakatar da shi daga aikata hakan.
Asali: Legit.ng