Home Back

Babban Dan Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

legit.ng 3 days ago
  • An shiga jimami bayan rasuwar babban ɗan tsohon gwamnan jihar Oyo, Cif Kolapo Ishola a yau Laraba a jihar
  • Marigayin mai suna Kunle Kolapo an tabbatar ya rasu ne da safiyar yau Laraba 3 ga watan Yulin 2027 a jihar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin babban ɗan tsohon gwamnan ne da ya mulki jihar daga 19991 zuwa 1993

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da mutuwar babban ɗan tsohon gwamnan Oyo, Kolapo Ishola.

Marigayin mai suna Kunle Kolapo ya rasu da safiyar yau Laraba 3 ga watan Yunin 2024.

Dan tsohon gwamna a Najeriya ya kwanta dama
Babban dan tsohon gwamnan Oyo, Kunle Kolapo ya rasu. Hoto: Olutoyin Adeyinka Eweje. Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadership ta tattaro cewa marigayin kafin rasuwarsa lauya ne kuma ya tsohon kwamishina a jihar.

Kunle ya rike mukamin kwamishinan ne a mulkin tsohon gwamnan jihar, Otunba Christopher Alao-Akala.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a bayyana musabbabin mutuwar babban ɗan tsohon gwamnan ba.

Har ila yau, iyalan basu fitar da wata sanarwa ba a hukumance kan babban rashin da suka tafka.

Tsohon gwamnan ya mulki jihar Oyo ne daga shekarar 1991 zuwa 1993.

Daga bisani, Isola ya rasu a ranar 9 ga watan Agustan shekarar 2011 yana da shekaru 77 a duniya.

Matashi ya hallaka mahaifinsa a Delta

A wani labarin, kun ji cewa wani matashi mai suna Ufuoma ya hallaka mahaifinsa wanda Fasto ne a jihar Delta a yau Laraba.

Marigayin mai suna Issac Umurie ya rasa ransa ne yayin da yake tsaka da bacci da tsakar daren yau Laraba 3 ga watan Yulin 2024.

Matashin har ila yau, ya farmaki mahaifiyarsa yayin da yake kokarin kare mijinta da kuma dakatar da shi daga aikata hakan.

Asali: Legit.ng

People are also reading