Home Back

Yadda ‘yan ta’adda ke cin karen su ba babbaka a yankunan Jihar Neja

premiumtimesng.com 2024/7/1
ABUJA TA DAGULE: Bayan garkuwa da mutum 11 a Dutse-Alhaji, ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum 23 a Bwari

‘Yan ta’adda da ‘yan bindiga sai ƙara yunƙura suke yi, su na ci gaba da kai munanan hare-hare a yankunan Jihar Neja da ke bakin ruwa, waɗanda suka haɗa da yankunan Lakpma da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Majiyoyi da dama sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan ta’adda sun sake afka wa yankunan wajen ƙarfe 3 na yammacin Laraba.

Sun yi kisa, sun arce da ɗimbin mazauna yankunan karkara da suka yi garkuwa da su. Sannan kuma sun gudu da shanu masu yawan gaske.

Aƙalla an bada rahoton kisan mutum bakwai, kuma an sace mutane da dama an yi garkuwa da su a Mazaɓar Bassa, kamar yadda wani shugaban wata ƙungiyar matasa a ƙauyen, mai suna Yusuf Dangana ya tabbatar.

Ya ce daga cikin waɗanda aka kashe, har da tsohon Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na mazaɓar.

Da farko dai ‘yan ta’adda sun kai farmaki a mazaɓar Bassa, inda suka kashe wani mai suna Saleh Jibo a Anguwar Usman. Daga can kuma suka darkaki Roro, inda a can ma suka kashe wani mutum mai suna Tanko.

Jibo wanda ke cikin waɗanda aka kashe a Bassa, ya sha tsallake hare-haren ‘yan ta’adda a baya.

“An taɓa yin garkuwa da matan sa da ‘yar sa, amma daga baya aka sake su bayan ya biya kuɗin fansa,” haka shugaban matasan ya shaida wa wakilin mu.

“Sau da dama ya sha tserewa idan ‘yan ta’adda sun kai masa hari.”

Daga nan ya kwashe iyalan sa ya bar ƙauyen, ya yi hijira zuwa wani sansanin ‘yan gudun hijira a Erena.

Dangana ya ce an yi wa Jibo yankan-rago a ranar Talata, lokacin da ya koma gida domin ya ɗebo kayan abinci a gonar sa, ya kai wa iyalan sa.

Farmakin Kwanan Nan:

A ranar Lahadi ‘yan ta’adda sun kai hari a Tungar Kawo cikin mazaɓar Erena, suka yi garkuwa da mutum 20, kuma suka tafi da ɗaruruwan shanu.

A wannan daren ne kuma suka mamaye ƙauyen Adogo Malam, cikin Ƙaramar Hukumar Mashegu, duk a Jihar Neja, suka kashe mutum shida.

Makonni kaɗan kafin ranar kuma sun kashe mutum shida suka jidi mutum 160 bayan sun yi wa mata shida fyaɗe a ƙauyen Kuchi, cikin Ƙaramar Hukumar Munya.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Neja, Garba Abdullahi, wanda wakilin mu ya kasa samu a waya, ya tura masa saƙon tes, amma har bayan haɗa wannan labari bai amsa ba, kuma bai rubuto masa ƙarin bayani ba.

People are also reading