PDP Ta Dauki Mataki Bayan Nade-Naden Gwamna Sun Bar Baya da Kura
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Jam’iyyar PDP a jihar Taraba ta buƙaci magoya bayanta da su yi taka tsan-tsan tare da kaucewa tayar da ƙura kan naɗe-naɗen da Gwamna Agbu Kefas ya yi a baya-bayan nan.
Jam’iyyar ta yi wannan roƙo ne biyo bayan yadda ake ta sukar tsofaffin ƴan siyasa da Gwamna Kefas ya naɗa muƙamai.
Wani jigo a jam’iyyar PDP a jihar, Hassan Kona ya nuna rashin jin daɗinsa kan nade-naden da gwamnan ya yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata hira da manema labarai a Jalingo, mai magana da yawun jam’iyyar a jihar, Andetarang Irammae, ya yi kira da a kwantar da hankula, cewar rahoton jaridar Tribune.
Ya kuma ba magoya bayan jam’iyyar tabbacin cewa jam’iyyar da gwamnatin Kefas sun damu da damuwarsu, rahoton jaridar The Sun ya tabbatar.
Jam’iyyar ta kawar da fargabar da ake ta samu a wasu ɓangarori na yadda aka yi watsi da waɗanda suka wahalta mata ta samu nasara a zaɓen shekarar 2023.
Ya bayyana cewa duk da Hassan Kona yana da ƴancin faɗar ra'ayinsa kan naɗe-naɗen da gwamnan ya yi a matsayinsa na ɗan jam'iyya, bai kamata ya tayar da hayaniya ba saboda Allah ne ke ba da mulki.
"Tabbas ya yi tunanin cewa za a sanya sunansa a cikin jerin, amma lokacin da ya gano babu sunansa, a wajensa wannan ita ce hanyar da zai nuna ɓacin ransa."
"Amma ya kamata ya sani cewa jam'iyyar tana da mambobi kusan miliyan ɗaya kuma ba zai yiwu a ba kowa muƙami ba a lokaci ɗaya."
"Sai dai a riƙa bayarwa a hankali a hankali, ina roƙo ga mutane irinsa da su kwantar da hankulansu sannan su ci gaba da marawa gwamnati baya."
- Andetarang Irammae
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya nuna adawa da shirin ƙirƙiro ƴan sandan jihohi da ake yi a ƙasar nan.
Gwamnan ya dage cewa hukumomin tsaron da ake da su a ƙasar nan na da ƙarfin magance ƙalubalen tsaro da ke addabar al’umma.
Asali: Legit.ng