Home Back

Sarkin Kano: Kotu Ta Umarci a Fitar da Muhammadu Sanusi II Daga Fadar Sarki

legit.ng 2024/7/4

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano ta Gidan Rumfa.

Kotun ta kuma umarci ƴan sanda da su tabbatar an dawo da duk wani haƙƙi da alfarmar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yake da su.

Kotu ta umarci a fitar da Sanusi II daga fadar Sarkin Kano
Kotu ta umarci a fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano Asali: Twitter

An tsige Aminu Ado Bayero ne a makon da ya gabata bayan amincewa da gyaran da aka yiwa dokar masarautun jihar Kano.

Bayan amince da kuɗirin dokar da majalisar dokokin jihar ta yi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaɓa hannu kan ƙudirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alƙalin kotun, mai shari’a S. A. Amobeda, wanda ya bayar da umarnin a ranar Talata ya bayyana cewa ya ba da umarnin ne domin tabbatar da adalci da wanzar da zaman lafiya a Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Asali: Legit.ng

People are also reading