Home Back

Zargin Kisan Kai: Kotu Ta Umarci Gwanatin Kano Ta Biya Ado Doguwa Diyyar N25m

legit.ng 2024/7/4
  • Dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa ya samu nasara a kotu a shari'arsa da gwamnatin jihar Kano kan zargin kisan kai
  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta wanke Ado Doguwa daga zargin bisa dalilai na rashin hujjoji da kuma rashin cancanta
  • Baya ga wanke Ado Doguwa, kotun ta kuma umarci gwamnatin jihar Kano da ta biya dan majalisar wakilan diyyar Naira miliyan 25

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke da zama a Abuja ta yanke hukunci kan zargin kashe mutane da gwamnatin Kano ke yi wa Hon. Alhassan Ado Doguwa.

A cikin takardar hukuncin da kotun ta yanke mai lamba FHC/ABJ/ABJ/CS/714/2019, an wanke Hon. Ado Doguwa daga zargin kisan kai da ake yi masa.

Dan majalisar wakila daga Kano, Alhassan Ado Doguwa
Kano: Kotu ta wanke Ado Doguwa daga zargin kisan kai@aadoguwa Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, Mai shari'a D.U Okorowo ya kuma nemi gwamnatin jihar Kano da ta biya Ado Doguwa diyyar Naira miliyan 25.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati da 'yan sanda ba su da hujjoji

Hon. Ado Doguwa, shugaban kwamitin majalisar wakilai kan man fetur, yana wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a majalisar tarayyar.

Gwamnatin NNPP ta jihar Kano ta gurfanar da Doguwa a gaban kotu ne kan zargin kashe mutane a lokacin zaben shugaban kasa na 2023.

Sai dai kotun ta ce gwamnatin jihar Kano da rundunar 'yan sanda sun gaza kawo hujjojin da za su tabbatar da zargin da suke yi wa Ado Doguwa, in ji rahoton PM News.

Zargin kisa: An kama Ado Doguwa

Rundunar 'yan sanda ta kama dan majalisar wakilan a Kano tare da gurfanar da shi gaban kotu kan zargin kisan kai.

Kotu ta bayar da shi beli, inda shi kuma ya nemi a bashi bayanin 'yan sandan da ya sa suka kama shi, tsare shi da kuma gurfanar da shi.

Tsohuwar gwamnatin APC a Kano ta shiga cikin lamarin a lokacin, ta jinginar da wannan tuhuma ta 'yan sanda tare da ba shi kariya.

Gwamnatin NNPP ta yi karar Ado Doguwa

Sai dai, jim kadan bayan karbar mulki, gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta sake gurfanar da Ado Doguwa gaban kotu kan zargin kisan kai.

Gwamnatin ta zargi dan majalisar wakilan da kashe mutane 15 wadanda da yawansu 'yan jam'iyyar NNPP ne a zaben 2023.

Sai dai Ado Doguwa ya maka Antoni Janar na tarayya (AGF), Sufeta Janar na 'yan sanda, gwamnatin Kano, Antoni Janar na Kano bisa zargin sun keta haƙƙoƙinsa na ɗan Adam.

'Yan bindiga sun kai hari Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyukan karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina, sun kashe mutane 22 da 'yan sanda hudu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, Abubakar Sadiq ya fitar, ya ce an yi nasarar kashe 'yan bindiga biyar a yayin wani artabu.

Asali: Legit.ng

People are also reading