Home Back

Shawara Daga Likita Kan Tiyatar Kara Girman Nono Da Mazaunai

leadership.ng 2024/5/18
Shawara Daga Likita Kan Tiyatar Kara Girman Nono Da Mazaunai

Sananniyar likitan nan, wadda take tashe a shafin sada zumunta; Dakta Na’ima Usman, ta gargadi mata kan yadda suke zuwa ana yi musu aikin tiyata, don kara girman mazaunai da kuma nononsu.

Daktar ta bayyana cewa, ya kamata mata su so kawunansu a yadda suke ba tare da kokarin canza wani bangare na halittarsu ba, duk da cewa; kowa na da ra’ayi da damar aikata dukkanin abin da yake so, amma a likitance; yin hakan ko shakka babu yana da illa kwarai da gaske.

Har ila yau, “magidanta maza ya kamata ku rika kula sosai tare da jin tsoron Allah, dalili kuwa sakamakon abubuwan da kuke fada wa matayenku ne; yasa suke bugewa da shaye-shayen magunguna, har ta kai ga zuwa a yi musu aikin tiyata, don kara girman nononsu ko duwawunsu.

Sannan, ya kamata maza su san cewa; duk matar da za ta haifa maka da ko ‘ya’ya, ko kadan ba ta cancanci raini ko wulakanci a wurinka ba, ko kallon wata sifa a jikinta ka kushe ko zaga ba.

Don haka, kamar yadda kowa ya sani ne; babu yadda za a yi a ce mace ta haihu daya-biyu, jikinta bai canza ba; domin kuwa ko babu komai za ta dauki ciki tsawon wata tara, bayan ta haihu kuma ta zo ta shayar da wannan da naka”.

Haka zalika, da yawa daga cikin mata, bayan sun haihu rayuwarsu take canzawa kacokan, wata ma wasu sabbin cututtuka ne ke shiga jikinta; kamar hawan jini, ciwon siga, ciwon zuciya da sauran makamakantansu.

Saboda haka, mata masu son sai sun birge mazajensu ko kuma suke fusata saboda gorin da suke yi musu; ya zama wajibi su lura su kuma kiyaye, domin kuwa wannan aiki da suke zuwa ana yi musu; baya ga barnar kudi da lokacinsu da suke yi, yana kuma cutar da lafiyarsu kai tsaye.

People are also reading