Home Back

Bayan Rasa Mulkin Kano, a Ƙarshe, Tinubu Ya Naɗa Nasiru Gawuna Shirgegen Mukami

legit.ng 2024/7/3
  • A karshe, dan takarar gwamnan a jihar Kano a karkashin jam'iyyar APC, Nasiru Gawuna ya samu mukami
  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Gawuna shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Bayero da ke jihar Kano
  • Wannan na zuwa ne bayan sauye-sauye a mukaman da ya yi a kwanakin baya wanda babu sunan Gawuna a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada Nasiru Gawuna babban mukami a Jami'ar Bayero da ke jihar Kano.

Tinubu ya nada Gawuna muƙamin shugaban kwamitin gudanarwar na Jami'ar bayan sake yin garambawul a mukaman.

Sauran ƴan kwamitim da ke karkashin Gawuna sun hada da Abubakar Dauda da Nora Alo da Ibrahim Obanikoro da kuma Musa Abbas.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading