Home Back

Rikicin Iran da Isra’ila a mahanga mai nisan zango, Daga Aliyu Ɗahiru Aliyu

premiumtimesng.com 2024/5/17
Rikicin Iran da Isra’ila a mahanga mai nisan zango, Daga Aliyu Ɗahiru Aliyu

Ita Isra’ila ta dogara da Amerika ne wajen faɗa da Iran. Ita kuma Amerika ba ta son faɗa da Iran, saboda ba ta da riba a ciki. Shi ya sa tun baya Amerika ke son ganin tashin hankali a Iran ta cikin gida, maimakon kai mata hari duk da za ta iya. To amma ana auna riba da asara ne wajen kowane yaƙi. Don haka ta ki tunkarar ta da yaƙin tun tale-tale, sai dai a ƙoƙarin zuga ‘yan ƙasar ko a saka takunkumi.

Sannan mafi yawan ‘yan Amerika a yanzu ba sa son Amerika ta shiga yaƙin da ba nata ba. Kuma a yanzu haka ‘yan ƙasar na ganin tsirarun Yahudawa ne ke juya Amerika. To idan ta shiga yaƙin nan za a ga ashe abin da ake faɗa ɗin da gaske ne. Daga nan Joe Biden zai faɗi zaɓe a banza. Shi kam ɗan siyasa ya fi damuwa da nasarar zaɓen sa akan komai. Don haka ba zai shiga yaƙin nan ba.

Sannan yaƙi tsakanin Amerika da Iran zai janyo tsadar man fetur a duniya. A zaton ka wa zai ci ribar hakan? Rusha ce! Ita kuwa a gurin Amerika da Rasha ta ci ribar yaki gwara an fasa yaƙin. Domin daga ƙarshe tattalin arzikin ta zai bunƙasa. Ka ga kenan ƙarfin Rasha ya ƙara yawa wajen tunkarar Amerikan kenan.

Duk duniya kuwa ba abin da Amerika ta tsana irin abin da zai sa Russia ta yi ƙarfi.

Wani babban dalili kuma shi ne, Iran na kewaye da ƙasashen da ba za su bawa Amerika damar kai mata hari ba. Afghanistan dai ko shigar ta ba za su yi ba, Pakistan ba za su ba su guri ba, Turkey ma haka, Iraq kuwa a hannun Iran take; sai dai ko Azerbaijan. Ita kuwa sai dai Amerika ta shige ta ta ruwa. To ganin kayan yaƙin Iran na ruwa da ta samu daga Rusha, yana nufin dubban sojojin Amerika za su mutu kafin su isa sansanin yaƙi. Wannan ma Amerika ba ta shirya masa ba a yaƙin da ba ta da riba.

Daga ƙarshe dai Isra’ila za a bari ta yi yaƙin ta. Ita kam ba ta da ƙawaye a Gabas ta Tsakiya da yawa. Dama Larabawa ne ƙawayen ta, su kuma ko don rikicin Gaza da shi ne ya janyo har aka zo nan ba, za su ba ta dama ba. Ƙarshe sai dai ta dinga kai hari sansanonin yaƙin Iran a wasu ƙasashen kamar Siriya. Wannan kuma ba yau aka fara ba. Ko kuma su kai hari ɗaya ko biyu a Iran mai nisan zango, wanda ba zai zamo cikakken yaƙi ba.

Wata babbar matsalar kuma ita ce, Iran tana da yara a kusa da Isra’ila waɗanda za su shigar mata yaƙin. Don haka yaƙin ya fi zuwa kusa da Isra’ila fiye da kusa da Iran. Wanda dama ribar yaƙi shi ne ya zamana ba a gidan ka ake ba. Sannan jama’a su sani Iran fa ƙasa ce ba ƙungiya ce kamar H***s ba ko raunana kamar Falasɗinu ba. Ƙasa ce mai kawaye da ƙarfin soja.

Daga ƙarshe dai yaƙin nan ba lallai ya yi zafi ba. Ina tunanin cewa za a yi tun da Isra’ila ce ta fara kai hari, kuma aka mayar mata da harin ramuwa, to a zo a yi sulhu. Daga cikin sulhun kuma shi ne sai a ce su fita daga Gaza. Wanda wannan kuma nasara ce ga Iran.

People are also reading