Home Back

Bauchi Za Ta Gudanar Da Zaɓen Shugabannin Ƙananan Hukumomi A Watan Agusta

leadership.ng 2024/6/29
Bauchi Za Ta Gudanar Da Zaɓen Shugabannin Ƙananan Hukumomi A Watan Agusta

Hukumar shirya zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bauchi (BASIEC) ta shirya gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 20 da suke jihar Bauchi ranar 10 ga watan Agustan 2024. 

Shugaban hukumar BASIEC, Ahmed Makama, shi ne ya sanar da hakan a hirarsa da manema labarai a ranar Juma’a, ya na mai bada tabbatar cewa hukumar ta shirya gudanar da sahihi, ingattaccen kuma karɓaɓɓen zaɓe ga kowani ɓangare.

Ya ce bisa yadda suke ƙunshe a dokoki, BASIEC ta samu umarnin gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi cikin kwanaki 60 masu zuwa.

A cewarsa, “Idan ku ka lissafi kwanaki 60 daga yau, zai kasance ranar 6 ga watan Agusta ne kuma ba ranar Asabar ba, sannan, yawancin lokuta an saba gudanar da zaɓuka a ranakun Asabar. Don haka mun tura zaɓen zuwa ranar 10 ga watan Agustan 2024.”

Ahmed Malama ya cigaba da cewa BASIEC za ta yi amfani da adadin masu rajistan zaɓe na hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) wajen gudanar da zaɓen, yana mai cewa su a ɓangarensu ba su cika ajiye jerin masu rijistan zaɓe ba.

Shugaban hukumar zaɓen ya kuma sanar da cewa an fara sayar da fom ɗin neman tsayawa takara ga dukkanin mutanen da suke da buƙata da su fito su sayi fom ɗin.

Daga bisani sai shugaban ya yi ƙira ga jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki da su bi dokokin da aka gindaya wajen taimaka wa shirye-shiryen gudanar da zaɓen domin ganin an yi cikin kwanciyar hankali.

Ahmed ya tunatar da ‘yan siyasa da jam’iyyunsu cewa lokacin fara gangamin yaƙin neman zaɓe zai fara ne kwanaki 30 da lokacin gudanar da zaɓen kamar yadda yake ƙunshe cikin doka. Sai ya shawarci masu ruwa da tsaki da su yi biyayya.

People are also reading