Home Back

Lauyan da Ke Kare Yahaya Bello Ya Watsa Masa Kasa a Ido Ana Cikin Zaman Kotu

legit.ng 6 days ago
  • Ɗaya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar Yahaya Bello a gaban kotu ya buƙaci alƙali ya amince ya daina wakiltar tsohon gwamnan
  • Adeola Adedipe ya gabatar da wannan buƙatar a yayin zaman kotun na ranar Alhamis, kan ƙarar da hukumar EFCC ta shigar da Yahaya Bello
  • Buƙatar da ya nema na zuwa ne bayan lauyan EFCC ya buƙaci alƙalin kotun da ya tsare lauyoyin tsohon gwamnan saboda sun kaso kawo shi gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani babban Lauyan Najeriya, SAN, Adeola Adedipe, ya buƙaci kotu da ta amince ya daina wakiltar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Lauyan ya miƙa wannan buƙatar ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis.

Lauyan Yahaya Bello na so ya daina wakiltarsa a kotu
Lauyan Yahaya Bello ya bukaci ya daina wakiltarsa a kotu Hoto: Alhaji Yahaya Bello Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce lauyan ya nemi wannan buƙatar ne a yayin zaman kotun na ranar Alhamis, kan ƙarar da hukumar EFCC ta shigar da tsohon gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yahaya Bello dai na fuskantar tuhuma guda 19 da suka haɗa da safarar kuɗade, zagon ƙasa da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma har kusan N80.2billion.

EFCC ta buƙaci a tsare lauyoyin Yahaya Bello

Biyo bayan rashin zuwan Yahaya Bello kotu, hukumar EFCC ta buƙaci alƙalin kotun da ya tsare lauyoyinsa saboda gaza cika alƙawarin da suka ɗauka na tabbatar da cewa ya halarci zaman kotun.

Babbar lauyan EFCC, Mista Kemi Pinhero, SAN, ya roƙi kotun da ta hukunta manyan lauyoyin biyu da a kodayaushe ke wakiltar tsohon gwamnan, inda ya dage cewa sun saɓa ƙa’idar aiki.

Lauyan ya nemi ya daina wakiltar Yahaya Bello

Da yake mayar da martani, Adedipe, SAN, ya shaida wa kotun cewa ba shi ba ne jagoran lauyoyin tsohon gwamnan inda ya musanta cewa ya ɗauki alƙawarin sanyawa Yahaya Bello ya halarci zaman kotun, cewar rahoton The Eagle Online.

Adedipe, SAN, ya ce tun da farko tawagar sa ta sanar da kotun cewa ba ta da masaniya kan inda tsohon gwamnan yake.

Ya ce dangane da yadda shari’ar ta ɗauki sabon salo, ba shi da wani zaɓi da ya wuce ya yi amfani da tanadin sashe na 349(8) na ACJA, 2015, ta hanyar janye wakilcin da yake yiwa wanda ake ƙara.

Sai dai, hukumar EFCC ta bakin lauyanta ta ce lokaci ya ƙure da lauyan zai nemi ya fice daga shari'ar.

An bayyana inda Yahaya Bello ya ɓoye

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban jigon jam'iyyar adawa ta PDP, Austin Okai, ya fallasa wurin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ɓuya domin kaucewa kamun EFCC.

Mista Austin Okai ya bayyana cewa yanzu haka Yahaya Bello na cikin gidan gwamnatin Kogi da ke Lokoja ya ɓoye

Asali: Legit.ng

People are also reading