Home Back

Ba mu yi mamakin binciken El Rufa'i a Kaduna ba - PDP

bbc.com 2024/7/6
Nasir El Rufa'i

Asalin hoton, NASIR ELRUFA'I/FACEBOOK

A Jihar Kaduna dake arewacin Najeriya, har yanzu ana ci gaba da tafka muhawara kan zargin tafka almundahana da Majalisar dokokin jihar ta yi wa tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai a shekaru takwas da ya yi a kan mulki.

Jamiyyar adawa ta PDP a jihar ta ce ta san za'a rina, kuma za ta zura ido ta ga irin matakan da gwamnatin APC a jihar za ta dauka.

Dan takarar gwamna a jam’iyar PDP a Kadunan a zaben 2023, Hon Isa Asiru Kudan, ya shaida wa BBC cewa, sun godewa Allah ba gwamnatin PDP ce ta yi binciken ba gwamnatin APC ce.

Ya ce,”An riga an tafka barna, kuma APC ce ta binciki APC, to amma da PDP ce ta yi wannan bincike da sai ace to akwai alamar tambaya, yanzu dai zamu jira muga abin da majalisar zartarwa za ta yi, idan ta yi abin da ya kamata kamar yadda ‘yan majalisar dokoki suka yi, zamu gani, idan ba ta yi ba kuma to.”

Sai dai a na ta bangaren jam’iyar APC mai mulki a jihar Kadunan, ta ce ba wani abin kunya game da wannan lamari.

Kakakin jam’iiyar APC a Kadunan, Salisu Tanko Husono, ya ce jam’iyyarsu ba ta gaji yin katsalandan a kan ayyukan majalisar ba.

Ya ce,”Majalisa hurumi ce mai zaman kanta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya ba su dama, kuma abin da duk ta yi ta na da ikon yi, kuma batun wannan bincike ma ai dan jam’iyyar PDP ne ya kawo batun a majalisar, to amma da ya ke aikin majalisar ne, dole ta yi abin da ya dace, kuma ma dai ai babu wanda ya fi karfin doka.”

Lamarin binciken tsohon gwamnan jihar ta Kaduna da majalisar ta nemi ayi dai ya janyo tsokaci daga mutane da dama ciki har masu sharhi kan lamuran siyasa inda wasunsu suka ce wannan lamari ya jefa gwamnatin APC cikin yanayi na tsaka mai wuya.

Dakta Haruna Yakubu Ja’i, masanin kimiyyar siyasa ne dake jami’ar jihar Kaduna, ya ce idan aka kalli abin da ke faruwa a Kaduna yanzu, za a ga duk dai guguwar siyasa ce da ake so a buga a 2027.

Ya ce,” Shi gwamna mai ci yanzu ya na cikin tsaka mai wuya, idan har ya zauna bai sa an yi bincike ba to gaba akwai matsalar da za ta shafe shi a siyasarsa, sannan kuma idan ya sa aka yi binciken to zai rinka samun matsala ta cikin gida a jihar tasa wanda kuma za ta hana sa gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.”

A yanzu dai za a iya cewa kallo ya koma sama inda ake jiran aji matakan da gwamnatin jihar za ta dauka domin kawo karshen wannan dambarwa.

A makon daya gabata ne dai majalisar dokokin jihar ta Kaduna ta bukaci gwamnatin jihar da ta nemi hukumomin yaki da cin hanci da rashawa su binciki tare da gurfanar da tsohon gwamnan da wasu mukararrabansa gaban kuliya, bisa zargin wawure sama da Naira Biliyan 420 na jihar.

People are also reading