Home Back

Gwamna Abba Ya Shiga Ganawar Sirri da 'Yan Majalisa da Masu Nada Sarki a Kano, Bayanai Sun Fito

legit.ng 2024/9/28

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abba KabirYusuf ya shiga ganawar sirri da ƴan majalisar dokokin jihar a gidan gwamnatin jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A ganawar da gwamnan ya shiga har da wasu masu riƙe da sarautun gargajiya da ake kyautata zaton masu zaɓen Sarki ne.

Gwamna Abba ya gana da 'yan majalisa a Kano
Gwamna Abba ya gana da 'yan majalisa a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf Asali: Facebook

Ana sa ran gwamnan zai sanya hannu kan ƙudirin dokar da majalisar dokokin jihar ta amince da shi tun farko a ranar Alhamis wanda ya rushe sababbin masarautu da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiro.

Idan Gwamna Abba ya sanya hannu kan wannan ƙudirin dokar, ana sa ran za a dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, wanda aka tsige a watan Maris ɗin 2020, cewar rahoton tashar Channels tv.

Sai dai har yanzu ba a san makomar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce Sarki Aminu Ado Bayero ba ya Kano a halin yanzu bayan da ya ziyarci Oba Sikiru Adetona, Awujale na Ijebuland, a ranar Laraba.

Gwamnatin tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso ta nada Muhammad Sanusi II, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), a matsayin Sarkin Kano na 14 a watan Yunin 2014.

Asali: Legit.ng

People are also reading