Home Back

Dansandan Da Ya Ki Karbar Cin Hancin Miliyan 150 Ya Samu Shatara Ta Arziki

leadership.ng 2024/10/5
cin hanci

Duk da hali na matsin rayuwa da wahalhalu da ake fama da su da gobe, bai hana wasu mutanen kirki aikata ayyukan kirki ba, kamar yadda aka samu wani jami’in dansanda da ya ki kabar cin hancin zunzurutun kudi har Naira miliyan 150, wanda kuma a dalilion haka ne ya samu kyautar fili a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Dama masu iya magana na cewa a ko da yaushe na Allah ba sa karewa, kuma shi dai alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza.

Rahotanni sun bayyana cewa, an karrama wannan Sufetan ‘yansanda mai suna (SP) Ibrahim Ezekiel Sini, ta hanyar bashi kyautar fili a Abuja. Wannan dansanda ya ki karbar cin hancin Naira miliyan 150 ne daga hannun wani dan kasuwa a Legas mai suna Akintoye Akindele, wanda kuma shi ne ya kafa ‘Platform Capital.

Kwamishinan ‘Yansandan Babban Birnin Tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, wanda ya ba da kyautar filin a madadin abokan aikin ‘yansandan, ya ce halin da SP Sini nuna ya sa rundunar ‘yansandan Nijeriya (NPF) alfahari.

Har ila yau, daya daga cikin wadanda suka shirya taron karramawar, Prince Chukwuemeka Okoye, Shugaban Kamfanin Begas Homes, ya ce halin da SP Sini ya nuna zama abin koyi kuma ya kamata ya zaburar da sauran jama’a da ‘yan Nijeriya su lura cewa rundunar ‘yansandan Nijeriya tana da mutane masu gaskiya da rikon amana.

A cewar sa, “Wannan hali da SP Sini ya nuna ba wai kawai ya kara wa kansa da kuma rundunar ‘yansandan Nijeriya kwarin guiwa ba ne, har ma da karfafa gwiwar wasu da dama da su tsaya tsayin daka wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma bin ka’idojin da’a. Wannan dabi’a tasa za ta ci gaba da zama abar yabawa, gami da nuni da cewa duk tsanani ana samun mutanen kirki.

“Ba a yi wannan karramawa kawai don yaba kyawawan halayen Sufeto Ibrahim Sini ba, sai don a yi nuna ga al’umma su yaba wa daidaikun mutane masu nagarta da halin kirki.

“Muna so mu nuna cewa rundunar ‘yansandan NIjeriya tana da jami’ai da suka kware, kuma suna da kwarin gwiwa wajen gudanar da aikin dansanda mai ma’ana kuma su zama abin koyi.”

Yayin da yake yaba wa halin Sini, Okoye ya ce taron na daya daga cikin sauran hanyoyin nuna godiya da suke da shi don halayensa na yabawa.

An ce dan kasuwar a cikin tuhumar ya yi watsi da zargin da aka yi masa na ya fata ba da ajiye Naira miliyan 50 a matsayin cin hanci ga tawagar masu binciken IGP wanda ke karkashin jagorancin SP Sini.
Ya kara da cewa “Kin karbar Naira miliyan 150 ya nuna tsoron Allah, gudun duniya da kuma kwarewar aiki, duk wadannan halaye ne da jami’i Ibrahim ya nuna.”

Idan dai za a iya tunawa, Akindele, wanda wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya ta tsare a gidan yari na Kuje, ana zarginsa da bai wa dansandan cin hancin Naira miliyan 150 domin ya janye binciken da yake yi akansa.

A cewar tuhume-tuhumen, an bayar da cin hancin ne ga ‘yansanda domin ba shi izinin tserewa kasar waje da kuma rubuta masa rahoto mai kyau bayan bincike.

An kama Akindele ne akan wata takardar korafi da Summit Oil International Limited ya mika wa shugaban ‘yansanda da ake zarginsa da damfarar kamfanin kudi Dala miliyan 5,636,397 da kuma wasu Naira miliyan 73,543,764.

A halin da ake ciki, SP Sini ya ce dalilin da ya sa ya ki amincewa da kudin cin hancin shi ne saboda ya gwammace ya samu natsuwa, ya ci gaba da yin gaskiya ga aiki da kare mutuncin rundunar ‘yansandan Nijeriya da kuma kiyaye mutuncinsa da na iyalansa.

People are also reading