Home Back

Neja: Tsohon Sakataren Gwamnati Ya Riga Mu Gidan Gaskiya, Gwamna Ya Tura Sako

legit.ng 2024/5/19
  • An shiga jimami bayan rasuwar tsohon sakataren gwamnatin jihar Neja, Kwamred Muhammad Adam Erena
  • Marigayin kafin rasuwarsa shi ne hadimin gwamnan jihar, Umar Bago ta bangaren da ya shafi kwadago a jihar
  • Gwamna Umar Bago ya tura sakon jaje ga iyalan marigayin inda ya yi addu'ar samun rahama da gidan aljanna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Gwamna Umar Bago na jihar Neja ya tura sakon jaje bayan rasuwar hadiminsa, Kwamred Muhammad Adam Erena.

Gwamnan ya bayyana mutuwar Erena wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar ne a matsayin babban rashi ga jihar.

Marigayin ya riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar ne a mulkin marigayi tsohon gwamna, Abdulkadir Kure.

Kafin rasuwar marigayin, shi ne hadimin gwamnan a bangaren da ya shafi ma'aikata da Kwadago.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Bologi Ibrahim ya sanar a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙwazo wanda ya sadaukar da rayuwarsa wurin ci gaban jihar.

Ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin inda ya ce dole su yi hakuri da hukuncin ubangiji wanda babu wanda ya isa ya yi tambaya kan haka.

Bago ya kuma roki Ubangiji ya yi masa rahama ya kuma saka masa da gidan aljannar firdausi.

Bayanai na nan tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading