Home Back

Kokarin yaki da cin-hanci da rashawa a Mali

dw.com 3 days ago
Mali | Assimi Goita | Sojoji | Cin-hanci
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali Assimi Goita

Kotun daukaka karar ta Mali za ta kwashe tsawon wata guda tana yin shari'a, domin hukunta wadanda aka samu da hannu wajen yi wa tattalin arzikin ta'annuti. Wadanda ake zargin da laifukan yin zamba cikin aminci da damfara da halatta kudin haram da yin sama da fadi da dukiyyar kasa, sun hadar da tsofaffin ministoci da ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa da kuma wasu zababbun shugabanin kananan hukumomi. Daga cikin mutane 181 da aka gurfanar ga misali, akwai tsohon shugaban majalisar dokokin kasar ta Mali a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita wato Issiaka Sidibé da tsohon babban sifeton kudin kasar Mamoutou Touré da aka fi sani da "Bavieux" da kuma shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Malin. Ana kuma zargin cewa, sun saci makudan kudi da yawansu ya kusan kai wa dala bilyan 17 na CFA. Sunayen da dama daga cikin tsoffin ministocin tsohon shugaban kasar Keita dai, wadnada suka hadar da tsohon ministan tattalin arziki da kudi Bouaré Fily Sissoko da kuma tsohon ministan sadarwa Mahamadou Camara.

Harkar EDMA ta makamashi da batun sayen jirgin sama na shugaban kasa da shugabannin kanan hukumomi da Cibiyar Gudanar da Taruka da Yin Bincike ta INPS, na daga cikin wuraren da za a bincika. Dangane da batun cinikin audiga da ake zargin tsohon shugaban kungiyar Manoma ta Kasa Bakary Togola da yin sama da fadi da kudade kusan biliyan 10 na CFA, ga dan fatutuka Abdoulaye Guindo kafa kotun ta mussammun ci gaba ne a fanin yaki da masu satar dukiyar kasa da kuma yaki da cin-hanci da karbar rashawa. Galibi a kan samu sama da fadi da dukiyar kasa a cikin kasahen Afirka ta hanyar bayar da kwangila saboda rashin sahihin tsari mai aldalci game da bayar da kwangilar, wanda sau da dama ba a  duba cancanta ko kwarewa. A wasu lokutan ma,a ana zargin bayar da kwangilar ba tare da yin aiki ba sannan ba a bibiya. Batun sake kwato dukiyar da aka sace ma, galiba ba a san yadda yake gudana ba.

People are also reading