Home Back

Copa America: Messi ya Cilla Argentina wasan ƙarshe bayan danƙara wa Canada kwallaye biyu a raga

premiumtimesng.com 2024/8/21
Copa America: Messi ya Cilla Argentina wasan ƙarshe bayan danƙara wa Canada kwallaye biyu a raga

Kaftin na babbar tawagar ƙwallon ƙafa ta Argentina Lionel Messi ya jagoranci kungiyyar zuwa wasan karshe na kofin kasashen kudancin America.

Argentina ta samu wannan nasarar ne bayan ragargazar Canada 2-0 a wasan kusa da na karshe.

Julian Alvarez ne ya fara zura kwallo a mintina na 22, daga bisa Messi ya zura ta biyu, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a mintina na 51.

Da wannan kwallon da Messi ya zura, ya zama ɗan wasa na biyu a duniya da yafi cin kwallo a wasannin kasashe bayan abokina hamayyarsa Cristiano Ronaldo wanda yafi kowa zura kwallo da guda 130,
Leo Messi 109 sa kuma Ali Daei mai 108.

Wannan dai shi ne karo na takwas da Messi ke jagorantar Argentina zuwa wasannin karshe a manyan kofunan duniya daban-daban.

Ya jagoranci ƙasar zuwa wasan karshe na kofin kudancin Amirka sau biyar, 2007, 2015, 2016,2021 da kuma na bana 2024, a kofin duniya ma, ya jagoranci Argentina zuwa wasannin karshe guda biyu, 2014 da kuma 2022 sai kuma wasan ƙarshe na Olympiics a 2008.

Argentina dai na jiran kasar da za ta yi nasara tsakanin Columbia da Uruguay, wanda zasu fafata a ranar Alhamis da ƙarfe 1 na safe filin wasa na Bankin Amirka.

Daga: Muhammad Suleiman Yobe

People are also reading