Shaguna Sun Kone Bayan Gobara Ta Tashi a Babbar Kasuwar Katako
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - An samu tashin gobara a kasuwar Katako da ke kan titin Kenyatta, a Uwani cikin birnin Enugu.
Gobarar wacce ta tashi a ranar Talata, ta lalata aƙalla shaguna biyar da ke cikin kasuwar.
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa cikin gaggawa jami'an hukumar kashe gobara suka kawo agajin gaggawa a kasuwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙoƙarin da suka yi wajen kashe gobarar ya sanya ba ta yaɗu zuwa sauran sassan da ke cikin kasuwar Katakon ba, rahoton PM News ya tabbatar.
Wani ma’aikacin kashe gobara da ya so a sakaya sunansa ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 9:45 na dare kuma nan take suka garzaya zuwa wajen.
Ya ce sun yi nasarar kashe gobarar ba tare da ta yaɗu zuwa sauran sassan kasuwar ba.
"Kusan shaguna biyar ne gobarar ta shafa a wannan babbar kasuwar. Ba zan iya cewa komai kan faruwar lamarin ba kasancewar ba ni ba ne shugaban hukumar kashe gobara."
- Wani ma'aikacin kashe gobara
Wani ganau ba jiyau ba mai suna Joe, ya bayyana cewa ya ga tashin gobarar ne bayan ƙungiyar ƙwadago ta dakatar da yajin aikin da take yi a faɗin ƙasar nan.
A cewarsa, wasu mutanen da ke makwabtaka da wajen sun garzaya zuwa kasuwar inda a cikin ƴan mintoci kaɗan jami’an kashe gobara suka iso suka kashe gobarar.
"Na godewa Allah da jami'an hukumar kashe gobara suka kawo agajin gaggawa, da ba domin hakan ba, da an yi mummunar ɓarna."
- Joe
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana matsalolin tashin gobarar da ta fuskanta da asarar da mutane suka yi cikin watan Mayun 2024.
Hukumar ta ce tashin gobara daban-daban da suka faru ya yi ajalin mutum takwas tare da lalata kadarorin da kudinsu ya kai Naira miliyan 31,650,700.
Asali: Legit.ng