Home Back

Yan Bindiga Sun Shiga Masallaci Sun Dauke Masallata Ana Sallar Dare a Jihar Arewa

legit.ng 2024/5/2
  • 'Yan bindiga sun kai sabon farmaki Gusau, babban birnin jihar Zamfara yayin da Musulmi suke tsakiyar yin sallar Tahajjud
  • An ruwaito cewa an kai harin a ranar Talata, kuma 'yan bindigar sun kutsa cikin Masallacin inda suka yi awon gaba da masallata da dama
  • Harin na ranar Talata shi ne na kusa-kusan nan da 'yan bindiga ke kai wa masallata yayin da suke ibada a cikin Masallaci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gusau, jihar Zamfara - A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani masallaci a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da masallata.

Rundunar 'yan sanda ba ta yi magana akan harin da aka kai Zamfara ba
Yan bindiga sun sace masallata da dama a Gusau yayin sallar Tahajjud. Hoto: @PoliceNG Asali: Twitter

Yan bindiga sun kai hari a Gusau

Jaridar Daily Trust ta gano cewa an kai harin ne a lokacin da Musulunci ke gudanar da sallar dare da aka fi sani da Tahajjud.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tahajjud wata Sallah ce ta musamman da Musulmi ke gudanar wa a kowanne kwanaki 10 na karshen watan Ramadan.

Harin na ranar Talata shi ne na kusa-kusan nan da 'yan bindiga ke kai wa masallata yayin da suke ibada a cikin Masallaci.

Hare-haren 'yan bindiga kan masallata

Sai dai har yanzu rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ba ta ce uffan kan harin ba, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

A karshen watan Fabrairu, akalla masallata 40 ne 'yan bindiga suka sace a wani Masallaci da da ke Tsafe, jihar Zamfara.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun ajiye baburansu a bayan gari, suka badda kamanni yayin da suka shiga garin.

Watan da ya gabata ma 'yan bindiga sun afka karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna inda suka kashe masallata biyu.

Asali: Legit.ng

People are also reading