Home Back

'Yadda ɗana ya mutu a ciki sa'o'i 6 sanadin masu damfara a intanet'

bbc.com 2024/7/5
Jordan DeMay da mahaifiyarsa  Jenn
Bayanan hoto, Jordan DeMay da mahaifiyarsa Jenn
  • Marubuci, Joe Tidy
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Cyber correspondent, BBC World Service
  • Twitter, @joetidy

Wata mahaifiya da danta ya kashe kansa sa’o’i 6 kacal bayan da ‘yan yaudara' suka kai barazanar wallafa hotunan tsiraicinsa ta intanet tana fafutukar wayar da kan jama’a kan alamarin.

Jordan DeMay ya mutu ne a shekarar 2022 bayan da wasu 'yan'uwa masu suna Samuel da Samson Ogoshi suka yaudare shi daga Lagos, inda suka yi kamar su wata budurwa ce mai kyau mai shekarunsa, sannan suka yi masa barazanar bata masa suna ta hanyar wallafa hotunan tsiraicinsa ta intanet.

A yanzu, mahaifiyarsa Jenn Buta, ta na amfani da shafin TikTok da danta Jordan ya bude mata don ta gargadi matasa kan irin wadannan mutane masu aikata miyagun laifuka, wadanda suka fi yawa a Najeriya - kuma hotunan bidiyonta sun samu masu bibiyarta fiye da miliyan .

'Yan sandan Najeriya sun shaida wa BBC cewa duk wani tunanin da ake yi a kan cewa ba su dauki al'amarin da muhimanci ba tamkar abin ''dariya'' ne.

'Matasan masu shekaru 22 da 20, sun rika kwarkwasa da matashin mai shekara 17,a shafin Instagram, inda suka aika masa da hotunan tsiraici kafin suka sa shi ya tura masu da hotunan kansa da ya yi tsirara.

Daga nan, sun yi barazanar bata masa suna idan bai ba su kudi ba domin kada su wallafa hotunan a shafin intanet

A lokacin da Jordan ya fada mu su cewa ba zai iya kara tura mu su da kudi ba kuma watakila ya kashe kansa, sai matasan suka ce : “ Gara ka yi haka cikin sauri - ko za mu sa ka yi shi.”

Asalin hoton, Nigeria Police

Samuel Ogoshi  da  Samson Ogoshi
Bayanan hoto, Samuel mai shekara 22 da Samson Ogoshi, mai shekara 20, da aka kama a Lagos, na zaman jiran hukuncin dauri a Amurka

A lokacin da aka tasa keyarsu Amurka, sun amsa laifin da ake zarginsu kuma suna zaman jiran hukuncin dauri .

Akwai kum wani mutum da ke kokarin ganin cewa ba a tasa keyarsa zuwa Amurka daga Nijeriya ba.

“Bai wuce sa'o'i kasa da 6 da Jordan ya fara magana da su har zuwa lokacin da ya kashe kansa,” Jenn ta shaidawa BBC, daga gidanta da ke Michigan, a arewacin Amurka.

“ Kamar suna amfani da wata takada da ke nuna mu su abinda za su ce a intanet''

" Kuma wadannan mutane su na amfani da abinda aka tsara dala-dala tare da matsin lamba''

" Kuma su na yin haka ne cikin sauri , saboda su koma kan wani da za su yaudara.”

Jenn Buta TikTok
Bayanan hoto, Mahaifiyar Jordanr, ta wallafa hotunan bidiyo da dama domin ta wayar da kan mutane

Wannan matsala ta fi shafar samari ko maza

A watan Afrilu, an kama wasu 'yan Nijeriya biyu bayan da wani yaro dan makarata a Ostriliya ya kashe kansa bayan da wasu suka yi bazanar bata masa suna

An kuma samu karuwa a yawan mutane da suka fuskanci wannan matsala daga Nijeriya a kasar Japan.

Haka kuma alkaluman miyagun laifuka da ake aikatawa a Amurka sun nuna cewa adadin masu aikata wannan laifi ya ninka fiye da sau biyu a bara zuwa dubu 26,700, inda yara maza akalla 27 suka kashe kansu a cikin watanni biyu.

A wannan mako, jami'an fasaha daga hukumar yaki da masu aikata laifi a intanet sun gana da jami'an hukumar kulla da laifukan intanet ta Burtaniya, domin su tattauna a kan yadda za su inganta hadin gwiwa kan laifukan intanet da suka shafi masu amfani da hotunan batsa domin bata suna

Hukumar NCA ta gargadi yara da makarantu kan karuwar da aka samu a yawan yaran da suka fuskanci bazarana a watan daya gabata .

Ta ce matsala ce da ake fuskanta daga kungiyoyi masu aikata laifuka da ke wasu kasashen yammacin Afrika da kuma Kudu maso gabashin Asiya.

'
Bayanan hoto, Shugaban hukumar yaki da masu aikata miyagun laifuka a shafin intanet a Najeriya Uche Ifeanyi Henry

Masu bincike kan harkokin tsaro ta intanet sun ce ana yawan alakanta laifukan da masu aikata zamba ta intanet da ake kira Yahoo Boys a Najeriya, wanda aka sanya wa suna bayan wata guguwar da ke da alaka da shafin imel na Yahoo a farkon shekarun 2000.

Kuma a farkon wannan shekarar, binciken da wata Cibiya da ke nazarin Intanet ta Amurka ta yi ya bankado yadda wasu 'yan Najeriya da ke amfani da TikTok da , YouTube da Scribd ke musayar bayyanai kan yadda za a bata wa matasa suna.

Daraktan cibiyar yaki da masu aikata laifi a intanet na Najeriya Uche Ifeanyi Henry ya shaidawa BBC cewa jami'ansa sun tashi tsaye wajan ''taka mu su birki'' kuma ya kare matakan da suke dauka domin shawo kan matsalar:

“Mutane na ganin cewa ba bu wani abin azo a gani da Najeriya ta yi domin sjawo kan matsalar kuma wannan abin dariya ,” in ji shi.

Kuma makudan kudaden da gwamnatin kasar ta kashe wajan gina helkwatar cibiyar yaki da masu aikata laifi a intanet ta zamani ya nuna cewa da gaske take wajan shawo kan matsalar

'Kasashe Makobta'

“Mun tashi tsaye wajan dakile ayuikan masu aikata wannan laifi," in ji Mista Henry.

"An gurfanar da dama daga cikinsu a gaban kuliya kuma an kama da yawa.

"Da dama daga cikin masu aikata wannan laifi sun koma da zama zuwa kasashe makobta saboda wannan mataki da muka dauka.”

Ana ci gaba da samun karuwa a yawan wadanda ake cin zalinsu ta intanet ta hanyar amfani da hotunan batsa kuma matsalar ta shafi matasa 'yan Najeriya.

Sai dai matsala ce da ke bukatar hadin kan kasashen duniya domin a iya kawar da ita

'Rashin aiki da Talauchi '

Duk da haka, Dr Tombari Sibe, daga wata cibiya da ake kira Digital Footprints da ke Nijeriya ya ce zambar cikin aminci ta hanyar amfani da hotunan batsa ta koma tamkar wani abu da ke samun karbuwa tsakanin matasan kasar masu amfani da intanet

“Abubuwan da suka janyo haka suna da alaka da zamantakewa da kuma tattalin arziki,” in ji sji .

“Akwai kuma matsalar rashin aiki da talauci.

" Wadanan matasa da ba su da abin yi ba su tunanin mumunan sakamakon da hakan zai haifar .”

'Fadarkarwa'

A yanzu, Jenn ta ci gaba da fafutukar wayar da kan mutane tare mahaifin Jordan.

Ta ce ta sami wasu iyaye da suka tuntubeta daga Amurka da Ostrliya da kuma Ingila wadanda ta taimaka mu su wajan yi mu su nasiha kan 'yayansu da suka mutu sanadin wannan matsala

“Ina samun sakoni a kowane lokaci daga iyaye da ke neman shawara saboda yaronsu ya fada hannun ma su aikata wannan aika aikar ," in ji ta.

Wani lokaci, suna son su fada mani abin da ya faru da yaronsu.

"Kuma wani lokacin suna cewa na gode saboda sun tuna da labarin Jordan kuma sun zo wurina don neman taimako."

People are also reading