'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Ta'addan IPOB a Jihar Ebonyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Jami'an ƴan sanda sun hallaka ƴan ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) mutum biyar a ƙaramar hukumar Ebonyi ta jihar Ebonyi.
Jami'an ƴan sandan sun hallaka masu tayar da ƙayar bayan ne a yayin wani artabu da suka yi.
Ƴan ƙungiyar ta IPOB sun kai farmaki ofishin ƴan sanda na Ishieke a cikin wata motar bas ƙirar Sienna mai launin shuɗi da misalin ƙarfe 9:30 na daren Laraba inda suka buɗe wuta kan ofishin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai ƴan sanda sun ci ƙarfinsu a wani artabu da ya ɗauki tsawon mintuna 30 ana fafatawa.
Hakazalika, jami’ai daga hedkwatar rundunar ƴan sandan jihar da ke Abakiliki da sojoji sun yi gaggawar kawo ɗauki bayan samun kiran gaggawa daga ofishin ƴan sandan na Ishieke.
Wata majiya mai tushe ta ce harbe-harben da aka yi ya tilastawa mazauna garin tserewa domin tsira da rayukansu.
"Ƴan bindigan sun je ofishin ƴan sanda na Ishieke sannan suka buɗe wuta. Ƴan sanda sun mayar da martani inda aka kwashe kusan tsawon mintuna 30, kafin sauran jami'an tsaro su iso wajen."
"Jami'an tsaro da dama ciki har da sojoji sun zo domin tunkarar ƴan ta'addan."
- Wata majiya
Rundunar ƴan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba kan aukuwar lamarin.
Ko da wakilin Legit Hausa ya tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi, ASP Ukandu Joshua, domin samun ƙarin bayani, ya bayyana cewa a jira shi zai kira daga baya.
"Eh ina wani abu a yanzu ka jira zan kira ka daga baya."
- ASP Ukandu Joshua
Sai dai, bai yi hakan ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta cafke wani babban ɓarawo mai suna Glory Samuel wanda ya ƙware wajen ɗauke-ɗauke.
Rundunar yan sanda tana zargin Glory Samuel da hannu a satar maƙudan kuɗaɗe da kayayyakin mutane da dama a jihar da ke yankin Arewa maso Gabas.
Asali: Legit.ng