Home Back

Gwamnonin Arewa-Maso-Yamma Sun Nemi Goyon Bayan MDD Kan Magance Ƙalubalen Yankin

leadership.ng 2024/6/26
Gwamnonin Arewa-Maso-Yamma Sun Nemi Goyon Bayan MDD Kan Magance Ƙalubalen Yankin

Gwamnonin yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya sun yi taro tare da tawagar Majalisar Dinkin Duniya, karkashin jagorancin mai kula da harkokin jin kai, Mohamed Malick Fall, a Abuja ranar Juma’a.

Manufar taron dai ita ce neman tallafi don tunkarar babban kalubalen ci gaban yankin.

Taron wanda Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma kuma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya jagoranta, ya samu halartar gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani, Injiniya Abba Kabir Yusuf na Kano, Mallam Umar Namadi na Jigawa; Mataimakin Gwamnan Sokoto, Alhaji Idris Muhammad Gobir, da Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal.

Taron wanda aka gudanar a zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja, ya mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi matsalolin tsaro, da talauci, da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Gwamnonin sun kuma bayyana damuwarsu game da karuwar shan miyagun kwayoyi, yawan mace-macen yara da mata masu juna biyu, da rashin aikin yi ga matasa.

Sun qara bayyana tasirin kalubale kamar gurbacewar kasa da sauyin yanayi kan noma, wanda kusan kashi 80 na al’ummar kasar ke dogaro da su.

Bugu da kari, gwamnonin sun jaddada illar matsalar karancin abinci mai gina jiki ga lananan yara.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma, ya jaddada buqatar samar da tsarin hadin kan yankin, inda ya ce, “Hanya daya da za mu iya shawo kan kalubalen Arewa maso Yamma ita ce hanyar da ake bi a yankin da ke bukatar mu hada kai ta hanyar haxin gwiwa. Ya kamata mu haxa karfi da karfe wajen yaki da talauci da rashin aikin yi, kasancewar manyan su abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a yankin.”

Sai dai kuma Babban Jami’in Kula da Ayyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya Mohamed Malick Fall, ya nuna farin cikinsa ga taron tare da tabbatar da aniyar Majalisar Dinkin Duniya na tallafa wa yankin na Arewa maso Yamma.

Ya bayyana muhimmancin rawar da yankin ke takawa wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) a Nijeriya, wanda hakan zai amfani daukacin nahiyar Afirka.

“Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya tana da kwarin gwiwar ganin kwakkwaran jagoranci da jajircewar Gwamnonin Arewa maso Yamma na inganta rayuwar al’ummarsu. Za mu ci gaba da tallafa wa gwamnati da al’ummar Arewa maso Yammacin Nijeriya. Tare, za mu ceto da kuma hanzarta ajandar 2030 don ci gaba mai xorewa a yankin, “in ji Fall.

Fall ya kara sanar da gwamnonin game da yadda Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da hankali wajen hanzarta cimma nasarar SDG ta fannoni shida: tsarin abinci, ilimi, kariyar zamantakewa da ayyukan yi, samar da makamashi, sauyin yanayi, da sauyi na dijital.

An kammala taron ne da yarjejeniyar samar da taswirar aiki, da tawagogin fasaha daga Majalisar Dinkin Duniya da na jihohi bakwai za su tsara, bisa tsarin tallafin Majalisar Dinkin Duniya ga yankin.

People are also reading