Home Back

Majalisar Zamfara Ta Dakatar Da Mambobi 8 Tare Da Rusa Kwamitocinta

leadership.ng 2024/4/29
Majalisar Zamfara Ta Dakatar Da Mambobi 8 Tare Da Rusa Kwamitocinta

Majalisar dokokin jihar Zamfara karkashin jagorancin Bilyaminu Moriki ta sanar da dakatar da wasu mambobin majalisar guda takwas.

In ba a manta ba, a baya-bayan nan, ‘yan majalisar 18 daga cikin 24 a makon da ya gabata sun sanar da tsige Kakakin Majalisar, Hon. Bilyaminu Moriki.

Sai dai kakakin majalisar ya sake bayyana a majalisar a ranar Litinin tare da manyan shugabannin majalisar ya kuma jagoranci zaman majalisar.

A yayin zaman, shugaban masu rinjaye na majalisar, Bello Mazawaje, ya gabatar da bukatar dakatar da ‘yan majalisar guda takwas, sannan mataimakin kakakin majalisar, Hon. Adamu Aliyu Gummi ya goyi bayan kudurin.

A cewar Mazawaje, ana zargin ‘yan majalisar takwas da hannu a yunkurin haifar da rashin fahimta a majalisar baya ga gudanar da zaman majalisar ba bisa ka’ida ba.

Don haka, Mambobin majalisar da aka dakatar sun hada da Hon. Bashiru Aliyu Gummi (Gummi 1), Hon. Bashiru Bello Sarkin Zango (Bungudu ta yamma), Hon. Shamsudeen Hassan Basko (Mafara ta Arewa), Hon. Faruku Musa Dosara (Mafara ta Kudu), Hon. Amiru Ahmad Keta (Tsafe ta yamma), Hon. Ibrahim Tukur (Bakura), Hon. Barista Bashiru Abubakar Masama (Bukkuyum ta Arewa), da Hon. Nasiru Abdullahi (Maru ta Arewa).

Daga nan ne shugaban majalisar ya sanar da rusa dukkanin kwamitocin majalisar.

 
People are also reading