Home Back

Yan majalisar Najeriya na son komawa tsarin mulki na wa'adin shekaru 6

bbc.com 2024/10/5
Yan Majalisar wakilan Najeriya

Asalin hoton,

Mintuna 4 da suka wuce

Majalisar wakilan Najeriya ta fara muhawara kan wasu kudurori da ke neman komawa ga tsarin yin wa'adin mulki guda na tsawon shekara shida ga shugaban kasa da gwamnoni da kuma shawawar samar da mataimakan shugaban kasa guda biyu daga bangaren arewaci da kudancin kasar

Kuma tuni kudirorin suka tsallake karatu na daya a majalisar wakilai kafin tsallakawa zuwa majalisar dattawa. Sai dai tuni wasu 'yan majalisar suka ce za su yaki kudirorin domin tabbatar da ba su yi nasara ba.

Majalisar wakilai ta ba da shawarar yin wa’adin mulki guda na tsawon shekaru shida ga shugabanni da gwamnoni sannan kuma ta koma kafa ofishin mataimakan shugaban kasa guda biyu daga yankin Kudu da Arewacin Najeriya. Kudirin doka guda shida da suka yi karatu na farko a zauren majalisar, ‘yan majalisar 35 ne suka dauki nauyinsu.

Yan majalisar wakilai 35 ne ke da'awar tabbatar da sabon sauyin na yi wa kundin tsarin mulki na shekarar 1999 kwaskwarima inda mulkn shugaban kasa na gwamnoni zai dawo wa'adi daya na shekara shida.

Me Yan Majalisar ke cewa?

Wasu daga cikin ƴan majalisar wakilan da ke goyan bayan kudurin irin su Injiniya Sagir Ibrahim Koki daga Kano, ya ce idan aka amince da ƙudurin zai baiwa gwamna ko shugaba ƙasar damar tsayawa ya gudanar da aikin sa cikin tsanaki ba tare da harkokin zabe ko siyasa sun dauke masa hankali ba.

“Hikimar wannan wa’adi na shekara 6 shi ne, da muka gabatar shi ne, muna ganin zai baiwa shgaban kasa ko gwamna ya yi abun da ya da ce, wand akum amu ba mu hango cewar lokacin ya yi musu kadan ba, a bisa dalilan da muke da su a ƙasa.

A hannu guda kuwa akwai wasu daga cikin ƴan majalisar wakilan da ke adawa da ƙudurin inda suka ce za su kalubalanci kudirin tare da tabbatar da cewa bai yi nasara ba.

Kabiru Alhassan Rurum na daya daga ckinsu inda ya ce samar da tsarn mulkin na falle daya ba komai zai haifar ba illa yasa mutum ya yi abin da ya ga dama saboda bashi da damar da zai koma mutane su sake zabar sa ba.

“ Idan aka ce zaai term daya ko shugabanci shekara 6, dga nan ka gama. Wanna zai yasa mutum ya yi abin da ya ga dama saboda bashi da damar da zai koma mutane su sake zabar sa ba, don haka zamu jira a gabatar da wanna kuduri a gaban majalisa.”

“Akwai yan majalisa iri na da yawa da basu gamsu ba kuma ba su yarda da wannan kuduri ba, domin kuduri ne da ya ke rushashe tun gabanin a gabatar da shi a gaban majalisar, don haka ba zamu amince da shi ba,” in ji Rurum..

Haka kuma a ɓangaren majalisar dattawan ƙasar kuwa tuni wasu daga cikin su, suka fara bayyana aniyarsu na goyon wannan kuduri, indai har majaliasar wakilan kasar ta mika musu kudurin gabansu, wanda kuma Sanata abdulrahman Kawu Sumaila na cikinsu, ya kuma ce tsarin shekru shidan ya fi kwanciyar hankali.

“Magana ta gaskiya, idan har yazo majalisar dattawa zan goyi baya wannan kuduri ina ganin ba karamin nasara ba ce za a samu a dimokaradiyar nan domin bana zataon wannan tsarin na 4 sau biyu na shekara 8 zai kai mu wani waje, shidan ma bata samun wa a wannan zabngon biyu akwai kashe kudi da zama na ɗar-ɗar da rashin kwanciyar hankali, Inji Kawu Sumaila

Sauran abubuwan da kudurin ya ƙunsa

Baya ga wa'adin mulki daya na shekara shida kudirin kuma ya kunshi samar da mataimakan shugaban kasa guda biyu daga arewaci da kudanci, akwai kuma Kudurin bukatar neman an gudanar dukkanin zabuka a rana daya tun daga na shugaban kasa da na yan majalisar tarayya da gwamnoni da kuma na yan majalisar jiha.

A daya kudurin kuma na ƙunshe ne da bukatar kammala dukkanin shari'iin zabe kafin rantsar da wa'adanda aka zaba.

Za a dai saurari ra'ayoyin jama'ar kasa bayan karatu na biyu, sannan ya kai ga majalisar dattawa idan kudurorin sun yi nasara har ya kai ga amincewar shugaban kasa.

People are also reading