Home Back

Malamai da Limamai a Arewa Sun Yiwa Masu Son Warware Rawanin Sarkin Musulmi Wankin Babban Bargo

legit.ng 2024/8/21
  • Majalisar malamai a Arewacin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga Sarkin Musulmi, mai martaba Alhaji Sa’ad Abubakar
  • Sun kuma soki duk wanda ke kokarin kawo tsaiko ga ci gaba da zamansa sarki a masarautar Sokoto, sun bayyana dalili
  • A baya, an bayyana maganganu da ke nuna yiwuwar ya warware rawanin Sarkin Musulmi na Sokoto ta hanyar dokar jihar

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kaduna - Majalisar Limamai da Malamai ta Jihar Kaduna ta sake jaddada cikakken goyon bayanta ga Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar.

Sakataren majalisar, Yusuf Arrigasiyyu, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Lahadi a Kaduna, kamar yadda Daily Nigerian ta tattaro.

Malamai sun ki a tsige Sarkin Musulmi
Malamai sun goyi bayan Sarkin Musulmi na Sokoto | Hoto: PIUS UTOMI EKPEI / AFP Asali: Getty Images

Da yake jawabi, Yusuf ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Muna tsaye kan goyn bayanmu ga Mai Martaba, Sarkin Musulmi kuma muna barranta da duk wani yunkuri na rage masa martaba ko kalubalantar wannan mukami mai girma.
“Masarautar Sokoto tana wakiltar tsarin hadin kai da kiyaye tarihin Musulman Najeriya, wanda ya watsu har a wasu jihohi.
“Muna ganin duk wani hari kan masarautar a matsayin cin mutunci da wulakanta kimarmu da addininmu.

A zauna lafiya, a bar Sarkin Musulmi ya yi mulkinsa

Ya kara da cewa:

“Muna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su aje makamansu su rungumi zaman lafiya, su gane muhimmancin rawar da masarautar take takawa wajen habaka hadin kai, fahimta, da zaman lafiya tsakanin Musulmai da kuma ‘yan Najeriya baki daya.
“Muna rokon mahukunta su girmama darajar masarautar da kuma mahimmancin tarihi da take da shi, tare da tabbatar da cewa ta ci gaba da zama fitila mai haske a fannin jagoranci da kuma hikima.”

Ya kuma ce, majalisar ta mika sakon gaisuwa da fatan alheri ga al’ummar Musulmi yayin da suke murnar shiga sabuwar shekarar Muslunci.

Zan karbi kowanne tsarin doka, Sarkin Musulmi

A wani labarin, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana shirinsa da burinsa na karbar kowacce doka da gwamnatin jihar Sokoto za ta gindaya.

Jagoran Musulmin Najeriya, ya bayyana hakan a ranar Talata a karamin zauren majalisar jihar Sokoto yayin kammala jin ta bakin jama'a kan gyaran dokar kananan hukumomin jihar.

Dakta Jabbi Kilgori, mamba a majalisar masarautar Sokoto kuma mai daya daga cikin masu naɗin sarakuna ne ya wakilci sarkin musulmi, rahoton Vanguard ya bayyana.

Asali: Legit.ng

People are also reading