Home Back

Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Abinci A Jihohi

leadership.ng 2024/4/29
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Rabon Abinci A Jihohi

Ministan gona, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa, ma’aikatar a wannan makon za ta fara rabon tan-tan 42,000 na kayan hatsi ga jihohi 36 da suke fadin Nijeria, biyo bayan amincewa da hakan da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi.

Kyari ya kara da cewa, ma’aikatar tana aikin hadin guiwa da hukumar samar da agajin gaggawa ta kasa (SEMA), hukumar tsaron farin kaya (DSS) domin tabbatar da kayan hatsin sun je wuraren da suka dace ba tare da an karkatar da su ba.

Ya shaida hakan ne a ranar Litinin a shafinsa na Tiwita, inda yake cewa, wasu karin ton 58,500 na shinkafa suma za a sake su a kasuwa domin saukaka wa jama’a samun kayan abinci.

“A irin wannan mayuwacin halin, ina jajanta wa wadanda suka samu kansu cikin matsin rayuwa a kasar nan. Na fahimci irin halin takuri da ake ciki, musamman kan yadda ake fasa rumbunan kayan abinci.

“Kan wadannan matsalolin da suka yi katutu, ina mai tabbatar wa jama’a kokari da azamarmu wajen shawo kan matsalar. Za mu fara rabon ton 42,000 na kayan hatsi biyo bayan amincewa da hakan da shugaban kasa ya yi, kowace jiha daga cikin jihohin da suke Nijeriya za su amfana da wannan shirn da zai fara daga wan-nan makon.

“Muna aikin hadin guiwa da NEMA da DSS wajen tabbatar da jama’an da suka dace ne suka amfana da kayan kuma ba a yi badakkala da su ba. Bugu da kari, ton 58,500 na shinkafa za a sake su zuwa kasuwanni domin daidaito da lamura,” ministan ya shaida.

 
People are also reading